Ina son sanya tufafin matata, cewar wani magidanci da ya caba ado da kayan matarsa

Ina son sanya tufafin matata, cewar wani magidanci da ya caba ado da kayan matarsa

  • Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan da hotunan wani magidanci sanye da kayan matarsa suka bayyana
  • Mutumin mai suna Brown Berg dai ya bayyana cewa yana kaunar sanya tufafin matarsa a rayuwarsa
  • Sai dai hakan da yayi ya burge mata da yawa inda suka bayyana shi a matsayin mijin da ya kware wajen iya soyayya

Wani magidanci ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu bayan ya caba ado da tufafin matarsa daga sama har kasa.

Mutumin mai suna Brown Berg ya je shafin Rant HQ Extension a Facebook inda ya wallafa hotunan da ya dauka sanye da tufafin matar tasa.

Ina son sanya tufafin matata, cewar wani magidanci da ya caba ado da kayan matarsa
Ina son sanya tufafin matata, cewar wani magidanci da ya caba ado da kayan matarsa Hoto: Brown Berg
Asali: Facebook

A cikin hotunan, an gano shi sanye da hula, shimi da kuma wandon uwargidar tasa inda ya cakare a kan kujera tare da kwaikwayon ta.

Magidancin ya kuma kalubalanci maza masu aure da su dauki hotuna sanye da tufafin matansu sannan kuma ya bukaci mutane da kada su yi masa shagube cewa shi ba dan shekara 70 bane.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta:

"Ina son sanya tufafin matata....
"Mazan gidan mu gan ku cikin tufafin matayenku.
"Dan Allah kada ku aibata surana. Dan Allah ni ba dan shekara 70 bane."

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane suka yi kan shigar tasa.

Sharon Ijuolachi Akpa ta ce:

"Dole ne gidan ka ya kasance mai dadin zama. Ci gaba da kasancewa cikin farin ciki."

Rukayya Ango ta ce:

"Kabiru Garba ya da sa kayan madame "

Aderibigbe Iyetunde

"Na son wannan .

"Watakila matar ta fusata ne, tabbass ganin haka zai tausasa zuciyarta da sanya murmushi a fuskarta "

Catherine Nwagwu:

"Matarsa da yaransa za su yi kewarsa idan baya gida,irin wadannan mazan suna maida kangon gida ya zama gida..ba wadanda ke hura hanci ba..na so haka yallabai "

Kwarya tabi kwarya: Babu laifi don mutum ya dage sai daidai da shi zai aura, tsohon dan majalisar Kano

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

A gefe guda, tsohon dan majalisar dokokin Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa ko kadan babu laifi don mutum ya dage kan auren wanda suke a aji guda a matsayin abokin rayuwa.

Jibrin, wanda ya wakilci mazabar Bebeji/Kiru na jihar Kano a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne a shafin Instagram a ranar Talata, 28 ga watan Disamba.

Hakan martani ne ga cece-kuce da ake yi kan dabi'ar mutanen arewacin Najeriya na son yin kwarya tabi kwarya musamman idan aka zo kan lamarin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel