Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa yara

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa yara

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisan kai a kan masu lalata da kananan yara 'yan kasa da shekaru 10
  • Kwamishinan shari'a kuma Atoni Janar na jihar, Dr Musa Adamu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai
  • Ya ce duk wanda aka samu da laifin zai fuskanci hukuncin ba tare da wani zabi ba

Jigawa - A ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, gwamnatin jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisan kai a kan masu lalata da kananan yara ta karfin tsiya.

Kwamishinan shari'a kuma Atoni Janar na jihar, Dr Musa Adamu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana cewa wadanda aka samu da laifin yin lalata da yara 'yan kasa da shekaru 10, za a yanke masu hukuncin kisan kai ba tare da mafita ba.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa mata
Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa mata Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Ya ce:

"Jimillar shari’a 196 aka samu yayin da aka shirya shawarwarin shari'a 178 kan korafe-korafen da aka samu.
"A farkon shekarar nan, Gwamna Mohammed Badaru Abubakar ya rattaba hannu a kan dokar hana cin zarafi, wacce ta tanadi hukuncin kisa ga masu lalata da mata ta karfin tsiya amma da zabin daurin rai da rai.
"Amma a baya-bayan nan, gwamnati ta kuma sanya hannu a dokar kare kananan yara, wanda ta yanke hukuncin kisan kai ga duk wanda ya haike wa yarinya 'yar kasa da shekara 10.
“A cikin jimillar shari’o’in, 90 sun kasance na fyade; 27 kisan gilla; luwadi yana da 31; garkuwa da mutane na da 18; lalata biyu; ayyuka na babban alfasha biyu; fashi da makami guda 20 yayin da laifuffukan karya dokar tuki ke da biyu.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 6, gwamnatin Katsina ta bayyana lokacin da za ayi zaben kansiloli

“Ma’aikatar ta gabatar da kara tare da kare jimillar kararraki 25 a gaban kotun daukaka kara, reshen Kano, sannan ta kuma kammala shari’ar laifuka 83 a gaban manyan kotuna takwas da ke Birnin Kudu, Dutse, Gumel Hadejia, Kazaure da Ringim. An sallami mutane 34 da ake tuhuma da laifuka 49 kuma an wanke su."

Kwamishinan ya kuma koka da jinkirin shari’ar da ake samu a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da ma’aikatar ke fuskanta, wanda a cewarsa ba wai a jihar Jigawa ba ne, rahoton Channels TV.

Adamu ya yi nuni da cewa za a iya rage matsalolin da ke da nasaba da jinkirin shari’ar laifuka ta hanyar amfani da fasahar da ta dace.

Matan Zamfara sun bada labarin yadda ‘Yan bindiga su ke kwanciya da su da karfi-da yaji

A wani labari na daban, matan da suka bar gidajensu saboda matsalar rashin tsaro a yankin Tsafe, jihar Zamfara, sun bayyana irin yadda ‘yan bindiga suke lalata da su.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

A ‘yan kwanakin bayan nan, mata da yara da dama sun tsere daga gidajensu saboda hare-haren da ‘yan bindiga suke kai wa a kauyukan yankin Tsafe.

Matan da ke wadannan kauyuka sun bayyana cewa ‘yan bindiga na tilasta masu kwanciya da su. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Larabar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel