Nan da Disamba 2022 za'a kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Nan da Disamba 2022 za'a kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

  • Ministan Sufurin Najeriya ya kai ziyara jihar Kano don ganin yadda aikin gina layin dogon Kano-Kaduna ke gudana
  • Amaechi ya bayyana cewa an baiwa yan kasar Chinan nan da karshen 2022 su kammala aikin
  • Wannan shine layin dogon na hudu da Gwamnatin Buhari zata kammala kafin karewar wa'adinta

Kano - Ministan Sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi ya bayyana cewa nan da karshen sabuwar shekarar da muke shirin shiga za'a fara amfani da layin dogon Kano zuwa Kaduna.

Ministan ya bayyana hakan ne a jihar Kano yayinda ya kai ziyarar ganin ido kan yadda aikin ke gudana, rahoton TheNation.

Amaechi ya kara da cewa Gwamnatin tarayya kawo yanzu ta zuba $400million wannan aiki kuma za'a kammala a kaddamar kafin wa'adin Shugaba Buhari ya kare a ofis.

Kara karanta wannan

An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar

Ya kara da cewa yan majalisar zartaswa sun sauya tsarin da aka yi na kashe $1.2billion kan aikin daga farko har karshe.

Yace:

"Mun zo ne domin gani ko yan kwangilan sun fara aiki kuma wani irin nisa suka yi saboda an basu nan da karshen Disamban badi ko watannin farkon 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nan da Disamba 2022 za'a kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi
Nan da Disamba 2022 za'a kammala layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi
Asali: UGC

Amaechi ya garzaya Daura daga Kano

Rahoton ya kara da cewa Ministan Sufurin ya karasa garin Daura daga Kano domin ganin yadda aiki ke gudana a Jami'ar Sufuri da ake ginawa a jihar Katsina.

Amaech ya bayyana rashin jin dadinsa kan irin ayyukan da masu kwangilan suka yi.

Ya kuma ce bayan kammalawa, kamfann kasar Sn ce zata gudanar da lamuran makarantar na tsawon shekaru biyar kafin ta dankawa gwamnati.

Yace:

"Masu kwangilan zasu rike makarantar na tsawon shekaru biyar amma ba su zasu fadi adadin daliban da za'a dauka ba, ma'aikatar ilmi ce zata fada."

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Amaechi makaryaci ne, Jonathan ya bar $28.6bn a asusun kasar waje na Najeriya, Omokri

A bangare guda, Reno Omokri, hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta batun cewa kudaden da tsohon shugaban ya bari sun kare bayan kimanin makwanni uku a 2015, Arise Tv ta ruwaito.

Omokri ya musanta wannan batun ta shafinsa na Instagram inda ya ce Amaechi ya dade yana nuna burinsa na tsayawa takara a matsayin mataimakin shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC.

Ya ce hakan yasa ya ke nemo karairayin da zai yi akan mulkin Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel