An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar

An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar

  • Ministan Buhari, Malam Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar nan ta korona a cikin wannan makon
  • Labarin da yake iso Legit.ng Hausa ya bayyana cewa, ministan na Buhari ya kamu da cutar ne bayan watanno suna wasan buya
  • Da yake bayyana halin da yake ciki, ministan ya kuma mika godiyarsa ga jami'an kula da lafiya bisa kokarinsu akansa

Abuja - Babban ministan birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar korona.

Ministan ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 31 ga watan Disamba.

An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar
An kuma: Ministan Buhari ya kama da annobar Korona bayan wasan buya da cutar | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Ya ce:

“Na kamu da cutar korona.
“Bayan tsawon watanni 21 (shekara daya da wata 9) muna wasan buya tsakanina da korona, a karshe cutar ta kama ni a ranakun karshe na 2021. Bayan jin zazzabi daga ranar 28 ga watan Disamba, sai na yanke shawarar yin gwajin Covid-19 a safiyar jiya.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

“Sakamakon gwajin da ya fito a safiyar yau ya nuna Ina dauke da ita. Yanzu ina cikin koshin lafiya, sai dai bushewar makoshi, zazzabi da mura. Ina samun kulawar likitoci sannan na killace kaina a gida.
“Ina jinjinawa Jami’an kiwon lafiya na birnin tarayya da wadanda ke kan gaba wajen yakar annobar kuma ina musu barka da sabuwar shekara ta 2022. Ina yiwa dukkanmu da muka harbu da cutar fatan samun lafiya.
“Kwararru sun sanar dani cewa nawa baida tsanani saboda nayi rigakafin korona biyu. Ina rokon wadanda basu yi rigakafin ba da su aikata haka.
“Nagode kuma barka da sabuwar shekara ga dukkanku.”

Ba wannan ne karo na farko da wani daga cikin jami'an gwamnatin Buhari suke kamuwa da cutar Korona ba.

Makwanni biyu da sauka gabata wasu mukararraban Buhari sun kamu da cutar.

Hadimin Buhari, Garba Shehu ya warke daga cutar Korona

A bangare guda, yanzu muke samun labarin cewa, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a ranar Laraba ya ce ya murmure daga cutar Korona.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta kame jami'in dan sandan da aka ga yana karbar cin hanci a wani bidiyo

Garba Shehu dai na daga cikin mataimakan shugaban kasa da suka kamu da annobar Korona a makon da ya gabata.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce:

“Na gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba ni saurin murmurewa daga Korona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel