Da duminsa: Gwamnan Bayelsa ya rantsar da matarsa matsayin alkalin babbar kotu

Da duminsa: Gwamnan Bayelsa ya rantsar da matarsa matsayin alkalin babbar kotu

  • Gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, ya rantsar da matarsa, Patience Zuofa-Diri, da wasu mutum 3 a matsayin alkalan babbar kotun jihar
  • Patience Zuofa-Diri, tare da wasu mutum uku da aka rantsar a gidan gwamnatin jihar, sun cika wasu sharudda tsaurara kafin samun matsayin
  • Gwamna Diri ya yi kira garesu da su bauta wa jama'ar jihar iyakar yadda za su iya kuma ya mika godiya ga NJC kan amincewa da zabin

Bayelsa - Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa ya rantsar da matarsa, Patience Zuofa-Diri, da wasu masana shari'ar uku a matsayin alkalan babbar kotun jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Baya ga matar Diri, sauran sabbin alkalan sun hada da tsohon magatakardan babbar kotun jihar Bayelsa, James Lookie, lakcara a fannin shari'a na jami'ar Niger Delta, Dr. Simon Amaduobogha da kuma lauya Christine Enegesi.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Da duminsa: Gwamnan Bayelsa ya rantsar da matarsa matsayin alkalin babbar kotu
Da duminsa: Gwamnan Bayelsa ya rantsar da matarsa matsayin alkalin babbar kotu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin basu rantsuwar kama aiki a matsayinsu na sabbin alkalai a gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa, Diri ya ce mulkinsa ya na bai wa fannin shari'a fifiko ganin irin rawar da suke takawa a al'umma.

Ya kara da tuna abun kunya irin kutsen da aka yi a gidan alkalin kotun koli, Mai shari'a Mary Odili, inda yayi kira ga hukumomin da suka dace da su dauka mataki kan masu hannu a ciki.

Gwamnan ya taya sabbin alkalan murna kan sabon mukaminsu da cigaban da suka samu, inda yayi kira garesu da su bauta wa mutane yadda ya dace, Daily Trust ta ruwaito.

Ya jinjinawa NJC, hukumar shari;a ta jihar, babban alkalin jihar da kuma alkalin alkalan Najeriya kan yadda suka amince da zabin babu bata lokaci.

Kara karanta wannan

Manyan Hafsoshin Sojin ruwa na hada kai da barayi wajen sace man fetur, Hukumar Navy

Ya ce an gano cewa sun dace da wannan ofishin bayan sun cika wasu manyan sharudda.

Matar babban basarake a Najeriya ta balle aurensu, ta bayyana dalilan ta

A wani labari na daban, Sarauniya Silekunola Naomi Ogunwasi, matar Ooni na Ife, ta balle igiyoyin aurensu da basaraken mai daraja ta daya. Wannan rade-radin ya bazu kan cewa ba ta tare da basaraken a yanzu.

Amma kuma, a sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, sarauniyar ta tabbatar da labarin mai bada mamaki inda tace a halin yanzu bata kaunar duk abinda zai hada ta da shi.

Wannan ne aure na biyu na basaraken da zai mutu tun bayan da ya hau karagar sarautar a 2015.

Asali: Legit.ng

Online view pixel