Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi

Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi

  • Bayan shekaru 14, hukumar EFCC ta sake gurfanar da Sanata Ibrahim Saminu Turaki, tsohon gwamnan jihar Jigawa a gaban kotu
  • Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta na zargin tshon gwamnan da laifuka 32 a gaban kotun
  • Ya gurfana a ranar 7 ga watan Disamba a babbar kotun tarayyar da ke Dutse inda ya musanta zarginsa da ake yi da wawurar N36 biliyan

Dutse, Jigawa - An cigaba da shari'ar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Saminu Turaki a babbar kotun tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, bayan shekaru goma sha hudu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Turaki ya bayyana a gaban kotun a ranar 7 ga watan Disamba inda ya ke fuskantar zargi 32 kan wawurar wasu kudi da suka kai N36 biliyan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Jami'an NSCDC sun gano gawarwakin matasa uku a Kogin jihar Benuwai

Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi
Bayan shekaru 14, an cigaba da shari'ar wawurar kudaden da tsohon gwamnan arewa ya yi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A shekarar 2007, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta damke tshon gwamnan kuma ta gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Mai shari'a Binta Murtala Nyako.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daga bisani an garkame shi a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da aka bayar da belinsa kan kudi naira miliyan dari tare da 'yan majalisar tarayya biyu, Bawa Bwari da Bashir Adamu, a matsayin tsayayyunsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekarar 2011, an mayar da shari'ar babbar kotun tarayya da ke Dutse bayan wanda ake zargin ya soki cewa kotun babban birnin tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar.

An sake gurfanar da shi a gaban kotun kan zargin aikata laifuka 32 a Dutse.

Mai shari'a Hassan Dikko aka mika wa shari'ar bayan Mai shari'a S. Yahuza ya yi ritaya.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna

An cigaba da sauraron shari'ar a Dutse a ranar 7 ga watan Disamban 2021 bayan ajiye shari'ar da aka yi na tsawon shekaru.

Bayan wannan cigaban, wanda ake zargin kuma tsohon gwamnan ya musanta aikata laifukan 32 da ake zarginsa da su.

Mai shari'a Dikko ya saka ranakun 24 da 25 na watan Fabrairun shekara mai zuwa domin cigaba da shari'ar.

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

A wani labari na daban, Malami ne ya tura bukatar a daura sabon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Fabrairun shekarar nan.

A wata murya wacce Daily Nigerian ta samo daga ‘yan cikin, an ji lokacin da jami’an EFCC su ke tattaunawa tare da wani Abdulbari Yusuf, kanin Rear Admiral kuma tsohon shugaban asusan sojojin ruwa mai ritaya, Tahir Yusuf, wanda yanzu haka ake shari’arsa akan rashawa.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

An ji Idris, wanda lauya ne ya na shawartar kanin Yusuf akan yadda za a ci nasara akan EFCC a kotun daukaka kara sannan ya na ba shi hanyar yashe kudade daga wani asusun banki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel