Matar babban basarake a Najeriya ta balle aurensu, ta bayyana dalilan ta

Matar babban basarake a Najeriya ta balle aurensu, ta bayyana dalilan ta

  • Sarauniya Silekunola Naomi Ogunwasi, matar babban basarake a jihar Osun, Ooni na Ife, ta sanar da rabuwar igiyar aurensu da basaraken
  • Mahaifiyar yarima Tadenikowa, dan da ta haifa wa basaraken, ta ce ya zama dole ta bar auren domin fara sabuwar rayuwa da rufe tsohon babi
  • Kyakyawar sarauniyar ta bukaci masu shiga lamarin da su janye kansu tare da duba darajar dan da ke tsakanin ta da basaraken

Osun - Sarauniya Silekunola Naomi Ogunwasi, matar Ooni na Ife, ta balle igiyoyin aurensu da basaraken mai daraja ta daya.

Wannan rade-radin ya bazu kan cewa ba ta tare da basaraken a yanzu.

Amma kuma, a sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, sarauniyar ta tabbatar da labarin mai bada mamaki inda tace a halin yanzu bata kaunar duk abinda zai hada ta da shi.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Da duminsa: Matar babban basarake ta balle aurensu, ta bayyana dalilan ta
Da duminsa: Matar babban basarake ta balle aurensu, ta bayyana dalilan ta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan ne aure na biyu na basaraken da zai mutu tun bayan da ya hau karagar sarautar a 2015.

Wallafar tsohuwar matar basaraken a shafin ta na Instagram shi ne kamar haka:

"Ina godiya ga Ubangiji kan ni'imar da yayi min a shekara uku da suka gabata na aure na. Har ila yau, ina godiya ga Ubangiji tare da tabbacin cewa komai daidai ne a lokutan jarabawa. Babu shakka na shiga gidan sarautar da zuciya mai kyau tare da soyayya."
"Wasu abubuwa da nake son a gane shi ne, idan mutum kuwa ya ji ba haka bane, ya taso da nashi hujjojin. Wannan hukuncin nawa na kara wa gaba bai bijiro ba saboda mai Martaba ya aura wata sarauniya. Kamar yadda da yawan mutane ake tunani, tun da na aure shi, ni kadai ce matar sa duk da akwai masu jan hankalinsa, hakan bai taba zama matsala ba.

Kara karanta wannan

Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa

"Ban taba tunkararsa ba a kan hakan saboda ni ya fara aure kuma ba hada mu aka yi ba kamar yadda wasu ke tsammani. Ban taba sanin faston da ake yadawa ta hada mu ba, shi ne ya hada ni da ita bayan na amince zan aure shi. Ina kuma biyayya ne saboda girmansa da nake gani.
"Ban taba yin ciki ba baya ga na Tadenikawo, da na shi ne ciki na na farko kuma akwai shaidar hakan. Yarinyar da ake cewa diyata ce, diyar 'yar uwata ce. Na yi iyakar kokari na wurin tabbatar da na zauna auren, na kan yi murmushi lokacin tsanani, amma na gane daga baya cewa, aiki daya gare ni, shi ne da yaro na. Sannan hukuncin Ubangiji ne karshe.
"Addini bai taba zama matsala tsakanin mu ba, ku tuna tattaunawa ta da News Central TV. A maimakon hakan, Mai Martaba ya na da wata irin fuska da ya ke son duniya ta san shi da ita kuma ita ce ta gaskiya. A yau, ina sanar muku da ketowar al-fijir din sabuwar rayuwa tare da rufe tsohon babin.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

"A yau, ni mahaifiya ce ga kyauta ta musamman ta Ubangiji. Ina sanar da cewa, daga yau na tashi daga matsayin matar Ooni na Ife ko sarauniyar Ile-Ife, amma sarauniyar mutane kuma mahaifiyar kyakyawan yarima.
"A irin wannan halin, akwai fusatattun mutane, ina rokon dukkan mai hannu a ciki da ya bari a zauna lafiya tare da tunanin akwai yaro namiji a tsakanin mu. Ina godiya ga duk masu yi min addu'a da masoya na.
"Har yanzu ina mayar da hankali kan ayyuka na, lamurran tallafi da kuma ma'aikata ta. A wannan sabuwar rayuwa, zan fi mayar da hankali ga Ubangiji".

Asali: Legit.ng

Online view pixel