Tashin Hankali: Jami'an NSCDC sun gano gawarwakin matasa uku a Kogin jihar Benuwai

Tashin Hankali: Jami'an NSCDC sun gano gawarwakin matasa uku a Kogin jihar Benuwai

  • Hukumar NSCDC ta sanar da cewa jami'anta sun samu nasarar zaro gawar wasu matasa uku a kogin jihar Benuwai
  • Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar, Mista Michael, yace hukumar ta samu rahoton batan matasan, waɗan da suka fita shagali bakin Kogin
  • Yace tun farko jami'an tsaro sun yi kokarin hana matasan gudanar da taro a bakin Kogin amma suka gagari jami'an saboda yawan su

Benue - Hukumar tsaro ta Civil Depence (NSCDC) reshen jihar Benuwai, ta gano gawarwakin wasu matasa uku a cikin kogin Buruku a jihar Benuwai.

Tribune Online tace wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar NSCDC, Ejelikwu Michael, ya fitar kuma aka raba wa manema labarai ranar Alhamis a Makurdi.

Hukumar NSCDC
Tashin Hankali: Jami'an NSCDC sun gano gawarwakin matasa uku a Kogin jihar Benuwai Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Yace matasan, waɗan da suka je shagali a kogin ranar dambe ta duniya, sun bata kuma aka gano gawarwakin su ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta faɗi babban kalubalen da ya dagula mata lissafi a 2021

Michael ya bayyana sunayen waɗan da lamarin ya shafa da; Andonso Iorliam dan shekara 20, Chiater Achi, dan shekara 18, da Aondongo Gbir dan shekara 30.

Abin da ya faru tun farko

Kakakin NSCDC ya kara da cewa hukumar ta samu rahoton tattaruwar daruruwan matasa a kogin Buruku suna gudanar da shagalin Carnival, wanda gwamnatin jiha ta haramta.

Leadership ta rahoto Mista Michael yace:

"Bayan samun wannan rahoton a ranar 25 ga watan Disamba, hukumar ta tura jami'anta tare da haɗin guiwar wasu hukumomin tsaro zuwa wurin domin dawo da doka da oda, kuma su hana taron."
"Amma adadin matasan ya nunka na jami'an tsaron yawa. Washe gari Lahadi 26 ga Disamba, mun samu rahoton batar wasu matasa, wanda daga baya muka tabbatar bayan gano gawarwaki uku ranar Litinin."

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

A wani labarin na daban kuma Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan bindiga da ya addabi Zamfara

Rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta sanar da cewa jami'anta sun samu nasarar kama kasurgumin dan bindiga, Sani Mati wanda aka fi sani da Mai Yan Mata.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Ayuba Elkana, yace ɗan bindigan ya shiga hannu ne yayin da suke kan hanyar kai hari da tawagarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel