Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

Muryar jami'in EFCC ya na sanar da yadda Malami ke kange masu cin rashawa ta bayyana

  • Bincike ya bankado yadda aka ji muryar wani jami’in EFCC ya na shawartar kanin tsohon jami’in sojin ruwa kuma mai kula da asusai a baya, Tahir Yusuf
  • Ya shawarci kanin Yusuf akan tuntubar ministan Shari’a, Abubakar Malami don ya yi magana da Abdulrasheed Bawa, shugaban EFCC don a sakar masa asusansa na banki su wawushi kudade
  • Abin mamakin shi ne yadda yanzu haka aka gano cewa Otal din Yusuf na Zaria da Kaduna wadanda EFCC ta rufe a baya, yanzu haka ta sake su sun ci gaba da aiki

Malami ne ya tura bukatar a daura sabon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Fabrairun shekarar nan.

A wata murya wacce Daily Nigerian ta samo daga ‘yan cikin, an ji lokacin da jami’an EFCC su ke tattaunawa tare da wani Abdulbari Yusuf, kanin Rear Admiral kuma tsohon shugaban asusan sojojin ruwa mai ritaya, Tahir Yusuf, wanda yanzu haka ake shari’arsa akan rashawa.

Jami'in EFCC ya fallasa yadda Malami yasa suka saki asusun bankin wadanda ake zargi, ya ke hada su da lauyoyi
Jami'in EFCC ya fallasa yadda Malami yasa suka saki asusun bankin wadanda ake zargi, ya ke hada su da lauyoyi. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

An ji Idris, wanda lauya ne ya na shawartar kanin Yusuf akan yadda za a ci nasara akan EFCC a kotun daukaka kara sannan ya na ba shi hanyar yashe kudade daga wani asusun banki.

“Idan yana da kudi a wani asusu da lambar BVN dinsa, ya yi gaggawar kwashe kudaden. Idan ya tura wa wani, EFCC za ta gano. Kawai ya ciro su ne ya sa a wani asusun na daban,” a cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yusuf ya kira sunan Malami a matsayin wanda ya ke fadi a ji a EFCC kuma ministan ya bayar da umarnin a saki “manyan asusan” da hukumar ta ke bincike a kai.

“Malami ne ke jagorantar EFCC, hukumar tana hannunsa. Da zarar Malami ya yi magana, za a saki asusan. Ana ta sakin asusan mutane da dama da ake zargi masu manyan matsaloli,” kamar yadda jami’in EFCC din ya ce.

Jami’in ya na magana ne akan batun sakin asusun kamfanin tsohon jami’in sojan ruwa, Aston, wanda EFCC ta daskarar da naira miliyan 114 yayin bincike.

Ya Kara da bayyana yadda antoni janar ya gabatar da wanda ake zargin ga lauyan don ya tsaya akan shari’ar.

“Eh, Malami ne ya gabatar da kai ga Ameh, don haka ba zai yuwu a ki sanar da shi halin da ake ciki ba,” inji jami’in EFCC din.

An samu bayanai akan yadda tsohon jami’in sojin ruwan ya yi iyakar kokarinsa don a saki asusansa lokacin Ibrahim Magu na shugabantar EFCC amma abin ya ci tura.

Sai dai binciken da Daily Nigerian ta yi ya nuna cewa ba a dade da sakin asusun ba don samun damar cire kudade kamar yadda jami’in EFCC din ya bayar da shawara.

Majiyoyi sun ce tsohon jami’in sojin ya na da alaka da manyan ‘yan siyasa, hakan ya sa EFCC ta saki otal dinsa na Kaduna da Zaria.

Daily Nigerian ta gano cewa Yusuf ne mai Grand Pinnacle Luxury Suites da ke Maiduguri.

Sai dai abun ban mamakin shi ne yadda Sanata Suleiman Abdu Kwari, shugaban kwamitin yaki da rashawa da laifukan kudade na majalisar dattawa ne ya ke rike da Otal din.

Yanzu haka kwamitin Kwari ne ke tafiyar da harkokin EFCC, ICPC da NFIU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel