Gwamnatin Buhari ta fadi adadin 'yan ta'adda da ta hallaka a 2021, da yadda ta yi hakan

Gwamnatin Buhari ta fadi adadin 'yan ta'adda da ta hallaka a 2021, da yadda ta yi hakan

  • Gwamnatin Buhari ta bayyana yadda ta samu nasarar karar da 'yan ta'adda sama da 1000 a shekarar nan ta 2021
  • Ministan yada labaru da al'adu na Najeriya, Lai Mohammed ya bayyana hakan a wani jawabin da ya yi a Legas
  • Ministan ya kuma bayyana matakan da gwamnati ta dauka domin tabbatar da tsaro da ingancinsa a Najeriya

Legas - A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta yi duba ga yakin da take yi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan a shekarar 2021, inda ta ce ta samu nasarar dakile ‘yan tada kayar baya da dama.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya yi jawabi ga taron manema labarai a Legas, ya ce an kashe ‘yan ta’adda a kalla 1000, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Minista ya jero tulin nasarori 100 da Gwamnatin Buhari ta samu a Najeriya a shekarar 2021

Minsitan yada labarai da al'adu ya magantu kan batun kashe 'yan ta'adda 1000 a 2021
Gwamnatin Buhari: 'Yan ta'adda 1000 muka hallaka a 2021, gwamnati ta fadi ta yaya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce yayin da mahara 22,000 suka mika wuya, an ceto fararen hula 2000 tare da kwace dimbin makamai da alburusai, ya kara da cewa an lalata wasu masana’antun sarrafa bama-bamai na ISWAP da ‘yan ta’addan Boko Haram.

Mohammad ya amince da cewa babban kalubalen da gwamnatin tarayya ta fuskanta a shekarar 2021 shi ne matsalar tsaro, kamar yadda Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, duk da kalubalen da ake fuskanta, sojojin sun samu nasarar cimma abin da ake bukata.

“Jarumanmu, a shiyyar Arewa maso Gabas a karkashin rundunar Operation HADIN KAI, hade da ayyukan motsi da ba na motsi ba, tare da dabarun soji, ya kai ga kashe ‘yan ta’adda sama da 1000, an ceto fararen hula 2000 tare da samun wadanda suka mika wuya daga ‘yan ta’adda sama da 22,000 harda iyalansu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta faɗi babban kalubalen da ya dagula mata lissafi a 2021

"Duk da girman kalubalen, sojojin mu sun ci gaba da aiwatar da ayyukansu."

Ta yaya za a dawo da zaman lafiya?

Ministan ya bayyana cewa, domin tabbatar da zaman lafiya a kasar, rundunar sojojin Najeriya (AFN) ta kaddamar da ayyuka daban-daban a fadin kasar.

A cewar Ministan, aikin sojan ya samu kwarin gwiwa ne sakamakon yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jajircewa, da kuma yadda ita kanta rundunar ta soji ta nuna jajircewa da kokarinta.

Ya bayyana cewa siyan “kayayyakin zamani ga rundunar soji” ya kuma taimaka wajen “daga matakin shirye-shiryen gudanar da ayyukansu, baya ga kara karfinsu.”

Hakazalika, ministan ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, inda ya bayyana yadda Najeriya ta kasance a shekarar 2021.

A fannin tattalin arziki, ministan ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar na kara farfadowa duba da yadda shekarar 2020 da annobar Korona ta lalata komai.

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja

A wani labarin, rahoton Daily Trust ya bayyana yadda Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta CNG ta koka kan yadda kashe-kashe, garkuwa da mutane, da rashin tsaro ya addabi yankuna a fadin kasar nan.

Daraktan Sadarwa na kungiyar ta CNG, Ismail Musa ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya mai da Najeriya yadda ya same ta a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Musa, wanda ya yi wannan kiran a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a ranar Laraba kai tsaye ta jaridar Vanguard, ya caccaki shugaban kasar Najeriya na yanzu kan yadda yake tafiyar da harkokin tsaro a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel