Babban kalubalen da ya dagula mana lissafi a 2021 shine rashin tsaro, Gwamnatin Buhari

Babban kalubalen da ya dagula mana lissafi a 2021 shine rashin tsaro, Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin tarayya tace babban kalubalen da ya hana ta sukuni a shekarar 2021 shi ne matsalar tsaro da ta kara ƙamari
  • Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace duk da haka gwamnatin Shugaba Buhari ta samu nasarori a 2021
  • Yace dakarun tsaron Najeriya suna aiki tukuru, kuma sun cancanci yabo da jinjina bisa sadaukarwan su wajen dawo da zaman lafiya

Abuja - Ministan yaɗa labaru, Alhaji Lai Muhammed, yace matsalar tsaro ce babban kalubalen da gwamnatin tarayya ta fuskanta a 2021.

Ministan ya faɗi haka ne ranar Alhamis a wurin taron manema labarai da aka shirya domin bayyana nasarorin gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a shekarar 2021 dake gab da kare wa.

Punch ta rahoto ministan na cewa duk da ɗumbin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a shekarar, rashin tsaro ya zame mata karfen kafa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fadi adadin 'yan ta'adda da ta hallaka a 2021, da yadda ta yi hakan

Ministan yaɗa labaru da al'adu, Lai Muhammed
Babban kalubalen da ya dagula mana lissafi a 2021 shine rashin tsaro, Gwamnatin Buhari Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Muhammed ya kara da cewa jami'an tsaron Najeriya sun samu nasarori sosai a yaƙin da suke da ayyukan ta'addanci domin dawo da zaman lafiya.

Wane nasarori FG ta samu a bangaren tsaro?

A cewar ministan, hukumomin tsaro sun samu nasarar hallaka yan ta'adda sama da 1,000, sun kubutar da mutane 2,000, sannan kuma yan ta'adda sama da 22,000 sun mika wuya tare da iyalansu.

Ya bayyana cewa an kwato makaman bindigu da alburusai da dama, kuma an ragargaza ma'aikatun haɗa bama-bamai da dama na yan ta'adda.

Daily Trust ta rahoto Ministan yace:

"Na amince kai tsaye cewa wannan shekarar cike take da kalubale, a 2021 babban kalubalen da ya dame mu shine rashin tsaro. Duk da haka, ga kuma matsalar tattalin arziki, FG ta yi muhimman ayyuka."

Kara karanta wannan

TRCN ta magantu kan shirin Buhari na fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

"Duk da yawaitar matsalar tsaro a ƙasa, jami'an tsaron mu ba su gajiya ba wajen kokarin shawo kan matsalar da ɗan kasafin da ake ba su."
"Suna bin mu bashin girmamawa da yabo bisa jajircewarsu da sadaukarwan su. Ba mu da kalmar da zamu yabe su da ita kan nasarorin da suka samu."

A wani labarin kuma Malami ya bayyana yadda shugaba Buhari ya ceci Najeriya daga tarwatsewa a shekarar 2015 bayan zaɓe

Ministan yace Buhari ya samu ƙasar nan tana tangal-tangal, kuma ya ceto ta daga kifewar tattalin arziki, wanda ka iya watsa kasar.

Malami yace shugaba Buhari ya yi abin da ba kasafai shugabanni ke iya yi ba cikin shekara ɗaya da hawansa karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel