'Yan Arewa sun magantu, sun bayyana yadda suka fi kaunar mulkin Jonathan fiye da Buhari

'Yan Arewa sun magantu, sun bayyana yadda suka fi kaunar mulkin Jonathan fiye da Buhari

  • Kungiyar 'yan Arewa ta bayyana irin halin da kasar nan ke ciki, inda tace sam ba ta jin dadin mulkin shugaba Buhari
  • A jawabin wani jigon kungiyar Arewa, ya bayyana yadda gwamnatin Jonathan ta fi ta Buhari da ke fama da rashin tsaro
  • Ya bukaci Buhari da ya mayar da Najeriya yadda ya same ta kowa zai fi samun hutu da jin dadi a ransa

Rahoton Daily Nigerian ya bayyana yadda Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta CNG ta koka kan yadda kashe-kashe, garkuwa da mutane, da rashin tsaro ya addabi yankuna a fadin kasar nan.

Daraktan Sadarwa na kungiyar ta CNG, Ismail Musa ya ce kamata ya yi shugaba Buhari ya mai da Najeriya yadda ya same ta a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Clark ga Lai Mohammed: Jonathan ne ya kori Boko Haram daga LGAs 14 a Borno ba Buhari ba

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari
'Yan Arewa sun magantu, sun bayyana yadda suka fi kaunar mulkin Jonathan fiye da Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Musa, wanda ya yi wannan kiran a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a ranar Laraba kai tsaye ta jaridar Vanguard, ya caccaki shugaban kasar Najeriya na yanzu kan yadda yake tafiyar da harkokin tsaro a kasar.

Ya ce:

“Abin da muke rokonsu a yanzu shi ne, kun san rayuwar dan adam na da mahimmanci kwarai da gaske tana da mahimmanci.
"Idan za ku iya yin wani abu, kai, idan za ku iya mayar da mu cikin rashin tsaro da kuka same mu da shi a cikinsa za mu iya jurewa ta yadda zamu ce ya mayar da mu yadda muke a zamanin Jonathan da muke kuka."

Babban kalubalen da ya dagula mana lissafi a 2021 shine rashin tsaro, Gwamnatin Buhari

A bangaren gwamnati, ministan yada labaru, Alhaji Lai Muhammed, yace matsalar tsaro ce babban kalubalen da gwamnatin tarayya ta fuskanta a 2021.

Kara karanta wannan

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

Ministan ya fadi haka ne ranar Alhamis a wurin taron manema labarai da aka shirya domin bayyana nasarorin gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a shekarar 2021 dake gab da kare wa.

Punch ta rahoto ministan na cewa duk da dumbin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a shekarar, rashin tsaro ya zame mata karfen kafa.

Muhammed ya kara da cewa jami'an tsaron Najeriya sun samu nasarori sosai a yaƙin da suke da ayyukan ta'addanci domin dawo da zaman lafiya.

A wani labarin, Wani Bawan Allah mai amfani da Facebook, mai suna Sirajo Saidu Sokoto ya bayyana cewa ya daina goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.

Malam Sirajo Saidu Sokoto ya fito kan shafinsa ya bayyana riddarsa daga tafiyar Muhammadu Buhari, yace ya koma goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya.

Da yake bayanin sauya-shekarsa a siyasa, Sirajo Sokoto yace ya shiga tsarin Kwankwasiyya ne a sakamakon dauke wasu ‘yanuwasa da ‘yan bindiga suka yi.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

Duk da ya na cikin masu kare gwamnatin Buhari a shafukan sada zumunta, Sokoto yace ba a taimaka masa a lokacin da aka yi garkuwa da ‘yanuwansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel