Minista ya jero tulin nasarori 100 da Gwamnatin Buhari ta samu a Najeriya a shekarar 2021

Minista ya jero tulin nasarori 100 da Gwamnatin Buhari ta samu a Najeriya a shekarar 2021

  • Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta jero irin nasarorin da ta samu a shekarar nan ta 2021
  • Alhaji Lai Mohammed ya bayyana wadannan cigaba da aka samu ne a wajen taron ‘yan jarida
  • Lai ya ce gwamnatin APC ta yi nasarar farfado da tattalin arzikin kasa da bunkasa sha'anin tsaro

Lagos - Mai girma ministan yaɗa labarai na kasa, Lai Mohammed, ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu a shekarar bana.

The Cable ta rahoto Alhaji Lai Mohammed a ranar Alhamis, 30 ga watan Disamba, 2021, ya kira taron manema labarai, inda ya fadi nasarorin da aka samu.

A cewar Ministan, duk da irin kalubalen rashin tsaro, gwamnatin APC ta yi kokari wajen yakar ta’adanci da farfado da tattalin arzikin kasar a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fadi adadin 'yan ta'adda da ta hallaka a 2021, da yadda ta yi hakan

“Abubuwan da muka yi shi ne mu tattaro manyan nasarorin da aka samu, shiyasa jerin yake da tsaro.”
“Mun kawo nasarori 100 da gwamnatin Buhari ta samu a shekarar 2021. Ba a auna nasara da kalubalen da aka fuskanta, sai dai yadda aka fuskance su.” - Lai
Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu nasarori gwamnati ta samu a 2021?

Rahoton yace jerin ya fara ne da nasarorin da jami’an tsaro suka samu a kan ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’ddan da ke tada kayar-baya a wasu jihohin Najeriya.

Sai kuma ayyukan tituna da aka yi, daga ciki akwai hanyar Nnewi-Uduma, Kano-Maiduguri, Vandeikya-Obudu, da Sokoto-Tambuwal-Jega-Kontagora-Makera.

A cikin jerin akwai gadoji dabam-dabam; gadar Ikom, gadar iyakar Najeriya-Kamaru, da gadar Neja.

Ministan yace an kawo tsare-tsare da suka inganta tattalin arziki; samar da aikin yi, da farfado da harkar ma’adanai. Sannan an gyara wasu filayen jirgin sama.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta faɗi babban kalubalen da ya dagula mata lissafi a 2021

Har ila yau, Lai ya ambaci nasarorin da aka samu a sha’anin noma da samar da ruwa. Manoma sun samu jarin miliyoyin kudi, an kuma ciyar da yaran makaranta.

Baya ga cigaba da aka gani wajen yakar rashin gaskiya a gwamnatin kasar, BBC ta rahoto Ministan yada labaran yace an fara wasu ayyukan titin jirgin kasa.

An kuma inganta yadda ake samun biza a Najeriya, sannan an gyara wasu gidajen yari. Sannan an ba matasa miliyan 1 aikin N-Power, an kuma dauki aiki a NNPC.

Masoyin Buhari ya yi ridda

Sirajo Saidu Sokoto ya na cikin masu ba gwamnatin Muhammadu Buhari kariya a dandalin Facebook, amma da alama ya iso tashar karshe a a motar Buhariyya.

Wannan mutumi yace tun da har ‘yan bindiga suka dauke ‘yanuwansa sai da aka biya kudin fansa, ba a taimaka masa ba, to ya koma goyon bayan Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel