Rikici ya barke a kotu yayin da aka hana ma'aikata shiga ofis saboda makara da safe

Rikici ya barke a kotu yayin da aka hana ma'aikata shiga ofis saboda makara da safe

  • An samu hargitsi a babban birnin tarayya Abuja yayin da wata kotu ta kulle kofar shiga ga ma'aikatan da suka makara zuwa aiki
  • Wannan lamari ya tunzura wasu ma'aikatan, inda suka ajiye motocinsu a kan hanya maimakon cikin harabar kotun
  • Ya zuwa yanzu dai ba asan abin da doka ta tanadar kan wadannan ma'aikata ba, amma dai an hana su shiga ofisoshinsu

Abuja - An samu hargitsi a kofar kotun daukaka kara da ke Abuja yayin da aka hana ma’aikatanta shiga harabar kotun da motocinsu.

Jami’an tsaro da ke bakin kofar sun ce shugabar kotun, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem ce ta umarce su da su kulle kofa domin hana ma’aikatan da ke zuwa bakin aiki a makare shiga harabar kotun da motocinsu.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

Kotu ta hana ma'iakata shiga ofis
Wata sabuwa: Rikici ya barke yayin da kotu ta hana ma'aikatanta shiga ofis saboda zuwa aiki a makare | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Saboda haka ne ma’aikatan da abin ya shafa da cikinsu har da daraktoci suka ajiye motocinsu a kofar shiga kotun, har zuwa babban titin da ya kai ga sakateriyar gwamnatin tarayya da kuma hedikwatar rundunar tsaro, wanda hakan ya shafi zirga-zirgar ababen hawa.

An tura jami’an ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru domin su taimaka wajen dakile cunkoson ababen hawa da kuma tsare motocin.

Jaridar The Nation ta ce an sanar da umarnin Mai shari’a Dongban-Mensem ne bayan zuwan ta ofis da safe kuma ta gano cewa yawancin ma’aikatan ba sa cikin ofisoshinsu, yayin da wasu ke shigowa bayan lokacin shiga ofis ya wuce a hukumance.

Wani jami'in kotun, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa:

“Yawancin ma’aikata sun saba zuwa a makare, yayin da wasu ma suka ce za su ci gaba da zuwa aiki ne shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

“Don haka ta umurci jami’an tsaro da su kulle kofa domin kada wadanda suka makara su shiga da motocinsu.
“Hatta motocin bas na ma’aikatan da abin ya shafa. Ka ga duk an ajiye su a waje.
"Duk da haka, ba mu da tabbacin irin hukuncin da za a yankewa ma'aikatan da suka yi kuskure ba daga karshe."

Punch ta rahoto cewa, daya daga cikin ma’aikatan kotun ya ce:

“Mai shari’a Dongban-Mensem ta yi wani abu makamancin haka a lokacin bikin Sallah amma da yawa daga cikin musulmi sun zarge ta da tsangwama. Don haka a yanzu ta yi a lokacin Kirsimeti don su san ba nuna wariya.
“An sanya mu sanya hannu kan rajistar ofis yayin da wadanda ba su zo ba za a ba su wasikun tuhuma. Gaskiyar ita ce, a lokacin hutu irin wannan da muke ciki, mutane da yawa suna tafiya garuruwansu ba tare da izini ba kuma ba sa zuwa wurin aiki.”

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Gwamna El-Rufai zai fara hana ma'aikatan da basu yi rigakafin Korona ba shiga ofis

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawarin daukar mataki kan ma'aikatan gwamnatin jihar da ba su yi allurar rigakafin Korona ba.

Wata sanarwa da gwamna El-Rufai ya fitar a shafinsa na Facebook dauke da sa hannun Muyiwa Adekeye, mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai ta bayyana dalilin daukar matakin.

Gwamnatin ta ce, daga ranar 31 ga watan Oktoba za a hana ma'aikatan gwamnatin da basu yi allurar rigakafi ba shiga ofisoshin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel