Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

  • Gabanin bikin sabuwar shekara, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta shirya ta dauki duk wata kasada mai alaka da Korona ba.
  • Gwamnati yi wannan sanarwar ne biyo bayan karuwar bullar cutar Korona s a kasar a 'yan kwanakin nan
  • A wani sabon mataki, FCT ta yi kira ga mazauna yankin da su bi duk ka'idojin kiwon lafiya kamar yadda ta hana yin taron ibada na jam'i fiye da mutane 50

Abuja - A wani bangare na kokarin ganin an kiyaye dokar lafiya, hukumar babban birnin tarayya Abuja ta sanar da haramtawa wuraren shakatawa da bukukuwa da majami’u na addini da ke da mabiya sama da 50 yin taro.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 25 ga Disamba, ta ce an sanar da matakin ne sakamakon sake barkewar Korona.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Annobar Korona
Sabuwar dokatr Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakazalika, gwamnati ta ce gazawar mazauna Abuja wajen daukar matakan kariya masu sauki abin damuwa ne ga lafiyar al'umma.

Gwamnatin, a cikin wata sanarwa da Sakataren, Sakateriyar Lafiya da Ayyukan Jama’a Dr. Abubakar Tafida ya fitar, ta yi kira ga mazauna Abuja da su dauki matakin kare kansu da ‘yan uwansu daga wannan annoba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sanarwar:

"Duk wani taro da ya wuce mutum 50 dole ne a yi shi a fili. An hana shagali a tituna. An hana duk wani shagalin kulob na dare da ayyukan da suka danganci haka a wannan lokacin.
"Ya kamata a iyakance taron jam'i na addini na cikin gida zuwa kashi 50 cikin 100 tare da cikakken bin matakan kariya na lafiyar jama'a kamar nisantar juna kamar nisan mita biyu da amfani da takunkumin fuska."

Hukumar ta ce ya zuwa ranar 24 ga watan Disamba mutane 2,591 ne, wanda ya kai kashi 1,028% na 252 da aka tabbatar sun kamu da cutar a watan Nuwamba 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja ta kama almajirai 104 masu kananan shekaru da aka shigo dasu

Gwamnatin ta ce duk mace-mace da aka samu daga Korona a cikin Disamba 2021 sun faru ne a daga mutanen da basu yi allurar rigakafin Korona ba.

Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona

Bayan bullar sabon nau'in Korona, kasar Kanada ta sanya dokar hana shigar yan Najeriya kasar a wani yunkuri na dakile yaduwar nau'in cutar Korona na Omicron, Daily Trust ta ruwaito.

Kasar ta Arewacin Amurka da ke samun kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan ne a safiyar yau Laraba 1 ga watan Disamba.

Ya zuwa yanzu, hukumomin Kanada sun haramtawa kasashe 10 shiga kasarsu saboda bullar sabon nau'in na Korona.

Kasashen sun hada da Afirka ta Kudu da Namibiya da Lesotho da Botswana da Eswatini da Zimbabwe da Mozambique da Najeriya da Malawi da Masar.

Ministan Sufuri na Kanada Omar Alghabra, ya ce ‘yan kasashen waje da suka je wadannan kasashe a cikin kwanaki 14 da suka gabata za a hana su shiga kanada na wani dan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

A wani labarin, Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar korona na Omicron da ke firgita kasashen duniya.

Hukumar ta ce an gano mutane biyu da ke dauke da nau'in cutar a halin yanzu. Dr Ifedayo Adetifa, Direkta Janar na hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.

NCDC ta ce an gano nau'in cutar biyu ne ta hanyar amfani da fasahar gano tsarin kwayar halita ta 'genomic sequencing'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel