Jami'an hukumar NSCDC guda 7 sun mutu a bakin aiki a jihar Neja

Jami'an hukumar NSCDC guda 7 sun mutu a bakin aiki a jihar Neja

  • Hukumar NSCDC reshen jihar Neja ta bayyana dumbin nasarori da kuma kalubalen da jami'an ta suka fuskanta a 2021
  • Kwamandan hukumar na jihar Neja, Haruna Zurmi, yace jami'ai bakwai suka mutu yayin da suke kan aiki a Neja
  • Yace hukumar ta samu nasarar warware matsaloli da dama, kuma ta baiwa ma su hakki hakkin su

Niger - Hukumar tsaro ta Civil Depence (NSCDC) ta bayyana cewa ta rasa jami'anta guda 7 yayin da suke kan aiki a jihar Neja cikin shekara daya.

Kwamandan NSCDC reshen jihar Neja, Haruna Bala Zurmi, shine ya bayyana haka ga manema labarai yayin da yake bayani kan ayyukan hukumar a shekarar 2021.

Daily Trust ta rahoto kwamandan na cewa hukumarsu ta samu korafe-korafe 1,578 da suka haɗa da na sata, bashi, rikicin filaye, cin mutunci da sauran su.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

Jami'an hukumar NSCDC
Jami'an hukumar NSCDC guda 7 sun mutu a bakin aiki a jihar Neja Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Nasarorin da NSCDC ta samu a 2021

A jawabinsa, Mista Zurmi yace hukumar da yake jagoranta ta samu nasarar kwato kuɗaɗe da suka kai kimanin miliyan N56.98m a cikin wannan shekarar dake gab da ƙare wa.

Haka nan kuma ya ƙara da cewa bayan samun nasarar kwato waɗan nan kuɗaɗe, hukumar ba ta tsaya nan ba, ta maida wa ainihin masu kudin kayan su.

Punch ta rahoto Zurmi yace:

"Mun kwato kimanin miliyan N56.98m, kuma mun damka wa ainihin waɗan da suke da kuɗaɗen."

Rawar da muka taka a bangaren rikici - Zurmi

Zurmi ya bayyana cewa hukumar ta miƙa korafi 147 ga sashin zaman lafiya da saɓani domin duba hanyoyin magance su.

Bugu da ƙari kwamandan yace hukumar ta sasanta korafi 1,428 daga cikin 1,578, yayin da ta kai guda 15 gaban kotu da kuma guda takwas da aka yanke wa hukunci.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan bindiga sun sake ƙona mutum kurmus a cikin mota a jihar Katsina

A wani labarin na daban kuma Mutane sun yi ta kansu yayin da yan bindiga sukamamaye mahaifar Sakataren Gwamnati Tarayya, Boss Mustapha

Yan bindiga sun matsawa mutanen kauyukan dake karkashin gundumar Garaha dake Hong, jihar Adamawa, inda SGF ya fito.

Mazauna yankin sun gudu baki ɗaya sai yan kaɗan domin tsira da rayuwarsu yayin da yan ta'adda suka mamaye yankunan da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel