Tashin Hankali: Yan bindiga sun sake ƙona mutum kurmus a cikin mota a Katsina

Tashin Hankali: Yan bindiga sun sake ƙona mutum kurmus a cikin mota a Katsina

  • A makonnin da suka shuɗe, wasu yan bindiga suka kona fasinjoji sama da 40 a cikin motar Bas a jihar Sokoto
  • Haka ta sake faruwa, inda a jihar Katsina wasu yan bindiga suka kona wani mutum ƙurmus a cikin motarsa a karamar hukumar Faskari
  • Matamakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, yace yan bindiga sun kashe mutane, kuma sun sace wasu a cikin mako ɗaya

Katsina - Mako biyu bayan abin da ya faru na ƙona fasinjoji a cikin mota a jihar Sokoto, wasu miyagun yan bindiga sun sake kona mutum a ƙaramar hukumar Faskari, jihar Katsina.

A cewar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, wanda shine mamba mai wakilaltar Faskari, sun kona mutumin da ransa a cikin motarsa.

Ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa wannan lamarin ɗaya ne daga cikin hudu da suka faru cikin mako ɗaya a yankin.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

Jihar Katsina
Tashin Hankali: Yan bindiga sun sake ƙona mutum kurmus a cikin mota a Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ɗan majalisar ya kara da cewa an kashe wasu mutane da dama sannan kuma aka yi awon gaba da wasu.

Premium Times ta rahoto a jawabinsa yace:

"Sun kai hari kauyen Kwakware inda suka sace mutum 17 mafi yawancin su mata ne. Washe gari suka tare direba, suka kashe shi, ta hanyar kona shi da ransa a cikin motarsa."
"A jiya Talata kaɗai, sun kashe mutum bakwai kuma suka yi awon gaba da wasu biyar. Kuma wurin da aka kai harin ba shi da nisa da madakatar binciken ababen hawa na sojoji."

Fusatattun mutane sun toshe manyan hanyoyi

Wasu fusatattun mutane a jihar Katsina sun toshe manyan hanyoyi kan yawaitar hare-hare yan bindiga da kashe mutane.

A makon da ya gabata, gwamna Aminu Bello Masari, ya jagoranci wasu dattawan jihar zuwa wajen shugaba ƙasa, Muhammadu Buhari, kan kashe-kashen mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

Shugaban ya shaida musu gwamnatinsa na kokarin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi arewa maso gabas da sauran sassan ƙasar nan.

A wani labarin na daban kuma Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, Matawalle

Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi yankunan jihar Zamfara, Bello Turji. ya nemi a sulhu da gwamati da sarakunan gargajiya.

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin sama da ƙasa sun ƙara ƙaimi kan yan bindiga bayan kotu ta ayyana su yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel