'Yan sanda sun ragargaji mafakar tsageru a Jigawa, an kame mutum 7

'Yan sanda sun ragargaji mafakar tsageru a Jigawa, an kame mutum 7

  • 'Yan sandan Jigawa sun kama wasu mutum bakwai bayan sun kai mamaya mafakar miyagu da ke kananan hukumomin Birnin kudu da Gwaram a jihar
  • Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamun nasu a ranar Talata
  • A cewarsa an samu nasarar ne sakamakon samamen da jami'an rundunar suka kai mabuyar tsagerun

Jigawa - Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutum bakwai a yayin wata mamaya da ta kai mafakar yan ta'adda a kananan hukumomin Birnin kudu da Gwaram da ke jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamun ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Dutse ranar Talata.

'Yan sanda sun ragargaji mafakar tsageru a Jigawa, an kame mutum 7
'Yan sanda sun ragargaji mafakar tsageru a Jigawa, an kame mutum 7 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shiisu ya ce an kama uku daga cikin wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 20 da 28 a kauyen Babaldu, karamar hukumar Birninkudu lokacin da tawagar 'yan sanda suka kai mamaya mafakar tsageru da ke yankin.

Kara karanta wannan

An kama wasu da suka bi dare suka sace shanu 2 a gidan wani a Jigawa

Ya yi bayanin cewa an samo sinki 85 na tabar wiwi, miyagun kwayoyi iri daban-daban guda 136, jarkokin sholisho 24 da wuka daya a yayin mamayar, rahoton The Nation.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa an samu daya daga cikin wadanda ake zargin da hannu a wani kisan kai da ya wakana a watan Agustan 2021.

Shiisu ya tuna cewa a ranar 6 ga watan Agusta da misalin karfe 7:50, wasu fusatattun mutane a kauyen Babaldu sun fatattaki wani barawon babur, inda suka kashe shi tare da cinna masa wuta.

A cewarsa, an kama sauran hudun ne a garin Sabuwar Gwaraw, karamar hukumar Gwaram, lokacin da 'yan sanda suka kai mamaya mafakar tsageru a yankin.

Ya ce an kama wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 20 da 40 dauke da sholisho.

Kara karanta wannan

Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda

A ruwayar The Guardian, kakakin 'yan sandan ya ce ana gudanar da bincike inda daga bisani za a mika su kotu.

Karya ne yan bindiga basu kai hari mahaifar sakataren Buhari a Adamawa ba – Yan sanda

A wani labarin kuma, rundunar yan sanda a Adamawa ta karyata wani rahoton yanar gizo da ke cewa yan ta'addan Boko Haram da yan bindiga sun kai hari mahaifar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Kakakin yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a rahoton cewa mutanen kauyukan Dabna da Kwabre a yankin Dubgwaba da ke karamar hukumar Hong sun bar gidajensu sakamakon hare-haren.

Mista Nguroje ya bayyana cewa hukumar yan sandar ta tura rundunar sashin da ke yaki da ta'addanci da masu garkuwa da mutane, sannan kuma ta tura jami'an bin diddigi zuwa yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel