An kama wasu da suka bi dare suka sace shanu 2 a gidan wani a Jigawa

An kama wasu da suka bi dare suka sace shanu 2 a gidan wani a Jigawa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargin barayin shanu ne a karamar hukumar Garki da Ringim
  • Jami’in hulda da jama’an rundunar, ASP Lawan Shiisu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a babban birnin jihar, Dutse ranar Litinin
  • A cewar Shiisu an kama barayin ne bayan masu shanun sun kai korafi akan yadda su ka bi dare ranar 14 ga watan Disamba su ka sace musu shanu

Jihar Jigawa - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa sun kama mutane biyu da ake zargin su na da hannu a satar wani sa a karamar hukumar Garki da ke jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar yan sandan, ASP Lawan Shiisu ya sanar da wakilin NAN a Dutse ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa dan majalisa ruwan wuta, sun dinga harbinsa babu kakkautawa

An kama wasu da suka bi dare suka sace shanu 2 a gidan wani a Jigawa
An kama barayin shanu 2 a Jihar Jigawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

A cewar Shiisu, an kama barayin ne bayan wani Nasiru Magaji ya kai musu rahoto akan yadda barayin su ka shiga har gidansa da misalin karfe 2:30 na daren ranar 14 ga watan Disamba.

‘Yan sanda sun bazana neman barayin bayan samun rahoton

Ya bayyana yadda ‘yan sandan su ka fara aiki bayan samun rahoton inda suka kamo su a kasuwar Wudil da ke jihar Kano, rahoton Daily Trust.

Kakakin ya kara da bayyana yadda aka kamo mutane biyu masu shekaru 30, inda aka gano daya mazaunin kauyen Jaya da ke Garki ne, dayan kuma Daware da ke karkashin karamar hukumar Ringim bisa zarginsu da alaka da laifin.

Za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike

Kara karanta wannan

Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte

A cewarsa, sauran mutane biyun da aka kama akwai mazaunin Jaya da ke karamar hukumar Garki shi kuma dayan dan kauyen Badage da ke karkashin Ringim.

Shiisu ya ce ana kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu don a yanke musu hukunci duk da yanzu haka ana kokarin kama sauran mutane biyun da ake zargin su na da alaka da satar.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel