'Yan bindiga sun yi wa dan majalisa ruwan wuta, sun dinga harbinsa babu kakkautawa

'Yan bindiga sun yi wa dan majalisa ruwan wuta, sun dinga harbinsa babu kakkautawa

  • A daren Alhamis, 23 ga watan Disamba wasu ‘yan bindiga su ka kai wa wani dan majalisa a jihar Delta farmaki
  • Sun harbi Honorabul Reuben Izeze sannan su ka yi garkuwa da direbansa sai dai daga baya sun sako shi
  • Lamarin ya zo da sauki don dan Majalisar bai mutu ba, yana wani asibiti inda ya ke jinya, duk da dai ba a bayyana sunan asibitin ba

Delta - ‘Yan bindiga sun harbi wani dan majalisar jihar Delta, Hon Reuben Izeze, mai wakiltar karamar hukumar Ughelli ta kudu a karamar hukumar Uvwie a ranar Alhamis, 23 ga watan Disamba.

Vanguard ta ruwaito yadda ‘yan bindiga su ka bude wa motar Izeze wuta bayan sun zo kusa a daren Alhamis din.

'Yan bindiga sun yi wa dan majalisa ruwan wuta, sun dinga harbinsa babu kakkautawa
'Yan bindiga sun yi wa dan majalisa ruwan wuta, sun dinga harbinsa babu kakkautawa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jami’an rundunar ‘yan sanda sun tabbatar da harin a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

Sai dai abin ban sha’awar shine yadda Izeze ya samu ya rayu amma dai yana asibiti ana kulawa da lafiyarsa, sai dai ba a sanar da sunan asibitin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An samu bayanai akan yadda suka yi garkuwa da direban dan majalisar daga baya kuma su ka sake shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da harin, The Sun ta kara da cewa.

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

A wani labari na daban, a kalla rayuka bakwai ne aka kashe kusa da wurin zaman sojoji a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina. 'Yan bindigan da suka yi wannan aika-aikar su ne da alhakin sace wasu mutane wadanda suka hada da mata da kananan yara, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Dalhatu Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majlisar jihar, ya sanar da Daily Trust cewa wannan ya na daga cikin farmaki hudu da suka fuskanta a cikin mako daya.

"Sun kai farmaki kauyen Kwakware inda suka sace mutane 17 wanda yawancinsu mata ne. Washegari sun tsare wani direba tare da kone shi a cikin motarsa.
"A ranar Talata kadai, sun kashe mutum bakwai tare da sace wasu biyar, wurin da suka yi barnar ba shi da nisa da matsayar sojoji," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel