Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte

Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte

  • Sakamakon luguden wutar da su ka sha, mayakan ISWAP sun birne ‘yan uwansu guda 77 a wuraren Marte, kamar yadda rahotannin sirri su ka nuna
  • Sojojin sama sun dinga auna wa mayakan wuta ta jiragen sama inda su ka ratsa sansanayen mayakan guda uku da ke kusa da tafkin Chadi
  • Lamarin ya auku ne a ranar 19 ga watan Disamban 2021 wanda jami’an tsaron hadin guiwa na kasashe karkashin Operation Hadin Kai su ka kai wa mayakan farmaki

Jihar Borno - Bayan shan luguden wuta da ragargaza, mayakan ISWAP sun birne ‘yan uwansu guda 77 a wuraren yankin Marte, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda rahotanni daga PRNigeria su ka nuna, an halaka mayakan ne sakamakon farmaki da sojojin saman Najeriya su ka kai sansanayen ‘yan ta’addan guda uku da ke wuraren tafkin Chadi.

Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte
'Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte, Bayan Shan Luguden Wuta Daga Sojoji. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

An samu bayanai akan yadda sojojin su ka lalata musu bindigogin yaki da babura da dama yayin farmakin.

An yi amfani da kayan yaki na ban mamaki

Wata majiyar sirri daga sojoji ta bayyana yadda yayin kai farmakin aka yi amfani da jiragen Super Tucano da sauransu wurin kai wa mayakan ISWAP din hari.

Kamar yadda majiyar ta shaida:

“Hare-haren da sojojin sama, karkashin Operation Hadin Kai da taimakon jami’an tsaron hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF), ya auku ne a ranar 19 ga watan Disamban 2021, a sansanayensu uku inda su ka halaka daruruwan ‘yan ta’adda a Arinna Sorro, Arinna Ciki da Arinna Maimasallaci da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.
“Bayan bincike da amfani da dabaru na sirri, sojojin sun kai farmaki wurin mayakan da su ka tsira daga harin baya wanda sojojin su ka kai Kusuma da Sigir.

“An samu bayanan sirri akan yawan ‘yan ta’addan da su ka koma sansanayen inda su ke kula da mayakan da aka ji wa raunuka a harin baya. An samu bayanai akan yadda mayakan ISWAP din su ka koma yankin don boye baburansu a duhun daji.”

Majiyar sirri ta bayyana yadda ISWAP ta birne mayakanta 77

Sai dai wata majiyar ta tabbatar da yadda mayakan masu rai su ka birne gawawwaki 77. Mayakan sun da su ka tsira sun koma don daukan gawawwakin kwamandojinsu da sauran ‘yan kungiyar.

A ranar Litinin su ka birne gawawwakin guda 77 a Tudun Giginya , wanda ya ke tsakanin Arena Chiki da Kwallaram cikin karamar hukumar Marte.

Yanzu haka Daily Nigerian ta gano yadda sauran mayakan da su ka ragu su ka koma Bukar Mairam da Yarwa Kura.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel