Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

Bakon lamari: Bidiyon dan sanda na raba wa matafiya buhunan shinkafa ya jawo cece-kuce

  • Wani jami'in 'yan sandan Najeriya mutumin kirki ya ja hankulan jama'a a shafin Instagram bayan da ya ba da buhunan shinkafa ga mutane a layi
  • A cikin wani gajeren faifan bidiyo, mutumin ya tsayar da wani direban keke napep da fasinjojinsa domin sanin yadda suka yi shagalin Kirsimeti
  • ‘Yan Najeriya da dama da suka mayar da martani kan faifan bidiyon sun ce sun yi mamakin cewa akwai jami’i mutumin kirki irin wannan a cikin ‘yan sandan Najeriya

Wani faifan bidiyo da @instablog9ja ya yada ya nuna wani dan sandan Najeriya yana wani abin da ba a saba gani ba yayin da yake yiwa matafiya kyautukan abinci a ranar dambe ta duniya.

A cikin bidiyon, bayan mutumin ya yi gajiriyar tattaunawa da su; Inda yake tambayarsu yadda suka gudanar da bikin Kirsimeti, ya bude bayan motarsa domin dauko kayan abinci.

Kara karanta wannan

Minista ya tona asiri, ya ce Jonathan bai bar wa Buhari komai a asusun Najeriya ba

Dan sandan kirki a Najeriya
A Najeriya: Dan sanda ya tsayar da mai a daidata sahu, ya masa kyautar buhun shinkafa | Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

Allah zai ci gaba da zuba maka albarka

Mutumin ya fito da buhunan shinkafa ya mika musu kowa guda. Har ma ya bai wa direban keke napep din da ke tuka su.

Mutanen sun yi mamaki matuka. A matsayin nuna godiyasu, jami'in ya sha jerin addu’o’i, suna masu cewa Allah ya saka masa da alheri, kuma Allah ya buda masa hanyar samun kudin shiga.

Kalli bidiyon:

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, bidiyon ya tattara maganganu sama da 1,000 tare da dubban dangwale.

Dan sandan Najeriya ne ya aikata haka?

Debargainer ya ce:

"To karbi kyautar ma tsoro zan ji.....hmmmm....kyauta daga masu bakin khaki."

maro_reigns ya ce:

"Me ke faruwa ne kam ina son sanin wannan sabon abu."

glowryhaa ya ce:

"A ina zan ga nawa Olopa Santa din."

Kara karanta wannan

Mu'ujizar Allah ce da kubutar da ni daga hannun yan bindiga, kwamishina ya magantu

scenteffect_ ya ce:

"Da alamu 'yan sandan sun yi taro, amma hakan na da kyau dai kam."

just.chelsea_ ya ce:

"Daga ina duk irin wadannan 'yan sanda na kirki suke."

__ololade__xx ya ce:

"Har yanzu akwai jami'an 'yan sanda nagari...kawai dai miyagu ne suke bata musu suna."

wf_jagaban said:

"Yara ne za su sha wahala daga ranar Litinin."

A kasar waje kuwa, jami'ai daga Sashen 'yan sanda na Ocala da ke Florida a Amurka, an gansu a cikin wani faifan bidiyo da ke rera taken Santa Claus.

A wani faifan bidiyo da Ayo Ojeniyi ya yada, wani jami’in dan sanda ya tare wata mata mai mota inda ya ce zai ba ta kudi $100 (N41,016). Da matar ta ji haka, sai ta tambaye shi ko da gaske ne zai yi hakan?

Bayan ya ba ta kudin, matar da ta kasa gaskata abin da ya faru a baya ta zabga kururuwa:

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

Wani bangare na faifan bidiyon ya nuna lokacin da wani jami'in daban ya tsayar da wani direban mota da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel