Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

  • Wani faifan bidiyo mai ban sha'awa ya nuna wasu jami'an 'yan sanda suna zagayawa don nuna murna da gabatowar bikin Kirsimeti
  • Tare da kaki a jikinsu suna ta raba $100 (N41,016) ga kowane mutum da suka yi arba dashi a bakin hanya
  • Da yawa daga cikin wadanda suka amfana da kyautatawar ‘yan sandan sun yi matukar mamakin ganin wannan karimci

Amurka - Jami'ai daga Sashen 'yan sanda na Ocala da ke Florida a Amurka, an gansu a cikin wani faifan bidiyo da ke rera taken Santa Claus.

A wani faifan bidiyo da Ayo Ojeniyi ya yada, wani jami’in dan sanda ya tare wata mata mai mota inda ya ce zai ba ta kudi $100 (N41,016). Da matar ta ji haka, sai ta tambaye shi ko da gaske ne zai yi hakan?

Kara karanta wannan

Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Yayin da yan sanda ke kyautar kudi
Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu | Hoto: @ayoojeniyi
Asali: Instagram

Kyautar kudi Kyautar kudi

Bayan ya ba ta kudin, matar da ta kasa gaskata abin da ya faru a baya ta zabga kururuwa:

"Na gode, Yesu!"

Wani bangare na faifan bidiyon ya nuna lokacin da wani jami'in daban ya tsayar da wani direban mota da daddare.

Ya tambaya ko mutumin ya taba haduwa da ‘yan sanda masu kirki. Bayan haka, ya sake mikawa mutumin $100 (N41,016).

Yada soyayya a cikin jama'a

Sun yi haka da yawa a cikin bidiyon. Nan take wani dan sanda ya tunkari wasu mata a wani wuri mai kama da wurin shakatawa. Da ya ba su kudin, sai suka fara tunanin wasa yake yi.

Yayin da ‘yan sanda ke shagaltuwa da yada soyayya ‘yan kwanaki kafin zuwan Kirsimeti, kyamarorin jikinsu suna daukar abubuwan da suke aikatawa na kirki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki a gidaje a Kano

Kalli bidiyon anan:

Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuceBidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Wani labarin, shahararrun ma'aurata a kafar Instagram, Masoud da Stephanie Shojaee, sun sa mutane magana yayin da matar ta yada wani gajeren bidiyonta da mijinta.

A cikin gajeren faifan bidiyon, an fito da matar ne daga cikin wata mota kirar Rolls Royce yayin da Masoud ya rufe idonta. A gabanta kuwa, ga wani jirgi mai zaman kansa.

Lokacin da aka bude idonta, sai matar ta rungume mijinta cikin murna da annashuwa. Ta rubuta cewa bayan shekaru 11, mijinta har yanzu ya san hanyar da zai ba ta mamaki da farin ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel