Allah ya nuna mu'ujizarsa yayin kubutar da ni daga hannun yan bindiga, Kwamishina ya magantu

Allah ya nuna mu'ujizarsa yayin kubutar da ni daga hannun yan bindiga, Kwamishina ya magantu

  • Kwamishina ya bayyana irin halin da ya shiga yayin da yan bindiga suka farmake shi da niyyar yin awon gaba da shi
  • Kwamishinan muhalli a jihar Kogi, Chief Victor Adewale Omofaiye, yace iko da mu'ujizar Allah ne ya tserad da shi daga sharrin maharan
  • Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar Kogi su rungumi zaman lafiya, soyayya da hakuri tsakaninsu yayin wannan lokacin na kirsimeti

Kogi - Kwamishinan muhalli na jihar Kogi, Chief Victor Adewale Omofaiye, ya bayyana cewa ikon Allah ne ya kubutar da shi daga sharrin yan bindiga.

Dailytrust ta rahoto kwamishinan na cewa mu'ujizar Allah ce ta tseratad da shi daga yunkurin yin awon gaba da shi a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2021.

Kwamishinan ya yi wannan furuci ne a Lokoja ranar Asabar, yayin wata gajeran tattaunawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Yan Shi'a sun halarci bikin Kirismeti tare da mabiya addinin Kirista a Zaria

Yan bindiga
Allah ya nuna mu'ujizarsa yayin kubutar da ni daga hannun yan bindiga, Kwamishina ya magantu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Haka nan Mista Omofaiye ya nuna tsantsar godiyarsa ga Allah bisa ceton rayuwarsa har ya kawo yanzun a raye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na yafe wa yan bindigan da suka so sace ni

Ya kuma ƙara da cewa ya yi imani da yin yafiya ga mutane, dan haka ya yafe wa tsagerun yan bindigan da suka yi yunkurin sace shi.

Kazalika kwamishinan ya yi kira tare da roko ga maharan su tuba su mika wuya daga ayyukan ta'addancin da suke yi domin ba hanya ce mai kyau ba.

Daga nan, ya roki al'ummar jihar Kogi su rungumi zaman lafiya, soyayya da kuma hakuri da juna yayin da kiristoci ke shagulgulan bikin kirsimeti a faɗin duniya.

Legit.ng ta tattaro.muke ceqa gwmanan Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin cewa duk wani ɗan ta'adda da ya sa kafarsa a jihar, ba zai fita da rayuwarsa ba.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

A wani labarin na daban kuma Pantami ya bayyana cewa ma'aikatarsa zata baiwa matasa horo musamman dalibai domun su yi gogayya a duniyar fasaha

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace za'a horad da karin matasan Najeriya sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani.

Wannan na ɗaya daga cikin amfanar da yan Najeriya za su yi da hadin guiwar ma'aikatar sadarwa da kamfanin Huawei Technologies Nigeria, inji ministan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel