Bayan Hadiman Shugaban kasa sun kamu da COVID-19, an bayyana halin da Buhari ke ciki

Bayan Hadiman Shugaban kasa sun kamu da COVID-19, an bayyana halin da Buhari ke ciki

  • Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana nan lafiya lau
  • Mai taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya tabbatar da cewa wasu hadimai sun kamu da COVID-19
  • Kawo yanzu babu abin da yake damun Muhammadu Buhari, kuma ya na cigaba da aikinsa a fadar Aso Villa

Abuja - Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina yace Mai girma Muhammadu Buhari ya na nan lafiya kalau.

Jaridar Daily Trust ta ce Mista Femi Adesina ya yi bayanin halin da shugaba Muhammadu Buhari yake ciki ne bayan wasu hadimansa sun kamu da COVID-19.

Adesina ya tabbatar da lafiyar shugaban kasar da aka yi hira da shi a shirin siyasa na Sunday Politics a tashar Channels a ranar 26 ga watan Disamba, 2021.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

Mista Adesina yace a halin yanzu an killace mukarraban na Muhammadu Buhari da aka samu sun kamu da cutar COVID-19, yace hakan ya nuna su ma mutane ne.

Mu ma mutane ne - Femi Adesina

“Abin nake son fada shi ne, hadiman shugaban kasa mutane ne. Za su iya kwantawa rashin lafiya. Duk abin da ke iya fadawa Bil Adama, zai iya faruwa gare su.”
“Don mu na hadiman shugaban kasa, bai nufin mun samu kariya daga wasu abubuwan.” - Femi Adesina.
Shugaban kasa
Buhari da amawalin COVID-19 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar Adesina, idan har akwai wata kwayar cuta da ta addabi al’umma, hakan na nufin za ta iya harbin kowa, hakan ya yi sanadiyyar da Garba Shehu ya kamu.

Garba Shehu na dauke da cutar, amma yace ba ta yi masa mummunan damka ba. Ina sa rai zuwa yanzu ya warke, domin tun Laraba ne, ba abin tada hankali ba ne.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya gwangwanje jami'an kan hanya da kyautukan kirsimeti a Kaduna

Ya lafiyar shugaban kasa?

“Ina tunani shugaban kasa ya na nan lafiya kalau, ya na cigaba da yin harkokin gabansa. Idan na-kusa a shi ya kamu, dole ya yi nesa da shi, sai ya warke.
“Saboda haka shugaban kasa (Buhari) ya na cigaba da harkokinsa da ya saba na yau da kullum.” - Femi Adesina.

A hirar ta sa, Adesina ya ki bayyana adadin wadanda suka kamu da COVID-19 a fadar shugaban kasa, yace likitan fadar ne kurum zai iya sanin amsar wannan.

An tsaurara matakan COVID-19 a Abuja

Gabanin bikin sabuwar shekara, gwamnatin tarayya ta bayyana tsaurara matakai domin gujewa yaduwar cutar COVID-19. A ranar Lahadi aka samu wannan labarin.

Gwamnati yi wannan sanarwar ne biyo bayan karuwar bullar nu'in Omicron na cutar COVID-19. An takaita taro a dakunan ibada da kuma gidajen shakatawa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel