Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki a 2023 - Buhari

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki a 2023 - Buhari

A ranar Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, Muhammadu Buhari ya kai ziyara zuwa birnin Maiduguri

Shugaban kasa ya ziyarci jihar Borno domin kaddamar da ayyukan gwamnati da na Muhammad Indimi

Buhari yace zai so wanda zai karbi mulki a hannunsa ya yaki rashin gaskiya, ya inganta tsaro da tattali

Borno - Muhammadu Buhari ya yi jawabi a jami’ar Maiduguri wajen kaddamar da cibiyar karatu da katafaren dakin karatu da Alhaji Mohammed Indimi ya gina.

Mai girma Muhammadu Buhari ya sake jaddada cewa zai bar mulki a lokacin da wa’adinsa ya cika a Mayun 2023, yace saura masa watanni 17 a kan karagar mulki.

Kamar yadda NTA ta rahoto shugaban kasar ya na jawabi kai-tsaye a jami’ar UNIMAID, yace zai so wanda zai gaje shi ya maida hankali sosai a kan wasu abubuwa uku.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

Na farko shi ne samar da tsaro, sai kuma shawo kan tattalin arzikin Najeriya. Haka zalika Buhari yace ya na so duk wanda zai gaje shi ya yi yaki da rashin gaskiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wahalar da na sha da hau mulki - Buhari

Shugaban Najeriyar yace ya sha wahala wajen yakar marasa gaskiya da ya hau mulki, yace a 2015 ya kafa kwamitoci da za su hukunta wadanda suka sace kudin kasa.

NTA ta rahoto shugaban kasar ya na cewa a zamanin da, masu mulki su na bayyana kadarori da kudin da suka mallaka kafin su hau mulki, da bayan su bar kujera.

Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari a Maiduguri Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

“Bayan mai rike da kujerar gwamnati ya sauka, zai nuna abin da yake da shi, idan an samu bambanci, sai a tsare shi ya yi bayani, ko ya tafi gidan kurkuku.”

Kara karanta wannan

Lai: Buhari ya samu mulkin Najeriya a yayin da ta ke tsaka da hargitsi

“A haka aka garkame ni na shekaru uku da watanni. Bayan gano ba ni da komai sai aka fito da ni. Daga baya na shiga siyasa in ji dadin zumbula babbar riga”

- Muhammadu Buhari

Buhari: Ana wasa da harkar noma a kasar nan

A jawabin na sa, Buhari yace ya yi mamakin da ya ji wani Farfesa ya na cewa 2.5% na arzikin filin da Ubangiji ya yi wa Najeriya kurum ake amfani da shi wajen noma.

An hurewa ‘yan kasar nan kunne da arzikin mai, sun watsar da harkar noma a cewar Buhari.

“Na yi gwamna, na yi Minista, na yi shugaban kasa na soja, amma maganar gaskiya ban san cewa 2.5% na filin Najeriya kurum ake nomawa ba.” – Buhari.

Najeriya za ta kashe N17tr a shekarar 2022

Dazu ku ka ji cewa abin da Sanatocin kasar nan 109 duk suka hadu kan Gwamnatin Tarayya ta batar a shekarar badi shi ne N17,126,873,917,692 bayan zaman karshe.

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

‘Yan Majalisar dattawa sun kara kasonsu da kansu da nufin su samu isassun kudin aiwatar da ayyukan da suka saba yi a duk mazabu a shekarar 2022 da za a shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel