Mutane da dama sun tsira yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka faɗa tarkon Mafarauta a Kaduna

Mutane da dama sun tsira yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka faɗa tarkon Mafarauta a Kaduna

  • Wasu tawagar mafarauta a yankin Birnin Gwari dake jihar Kaduna sun mamayi yan bindiga sun bude musu wuta
  • Wani mazaunin kauyen Udawa, yace Mafarautan sun samu nasarar kubutar da mutum 9 daga hannun yan ta'addan
  • Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan lamarin, domin ba ta ji daga Mafarautan ba zuwa yanzu

Kaduna - Mafarauta a ƙauyen Udawa dake karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna sun samu nasarar kama ɗan bindiga a dajin dake hanyar Birnin Gwari.

Dailytrust ta rahoto cewa Mafarautan sun ceto mutum 9 daga hannun yan ta'addan, a wani hari kan yan bindiga da suka ƙaddamar.

Rahoto ya bayyana cewa tawagar mafarautan sun ɗana wa yan bindigan tarko, kwanaki kaɗan bayan sace dandanzon matafiya a kan hanyar.

Mafarauta
Mutane da dama sun tsira yayin da wasu tsagerun yan bindiga suka faɗa tarkon Mafarauta a Kaduna Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Su wa Mafarautan suka ceto?

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun yi awon gaba da baban sarki a jihar Arewa

Wani shugaban al'umma, Muhammad Umaru, ya shaida wa manema labarai cewa mutanen da Mafarautan suka kubutar sun fito ne daga ƙauyen Udawa.

Yace:

"Mafarautan sun samu nasara a Operation ɗin da suka fita saboda sun ceto mutum 9 daga hannun yan bindigan, kuma sun kamo mutum ɗaya a raye."

Yadda lamarin ya faru?

Legit.ng Hausa ta gano cewa Mafarautan ne suka bude wa yan bindigan wuta, wanda hakan ya tilasta musu barin mutanen dake hannun su, suka tsere.

Umaru yace baki ɗaya mazauna yankin sun yi farin ciki da wannan nasara, inda ya kara da cewa da za'a samarwa waɗan nan mafarautan kayan aiki da sun kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga a yankunan.

Haka nan kuma ya yaba wa hukumomin tsaro bisa ɗaukar mataki kan yan ta'addan bayan hare-hare biyu da aka kai makon da ya shuɗe.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi ta kansu yayin da Yan bindiga suka bindige Basarake har lahira a Kaduna

Shin yan sanda sun samu rahoto?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, yace har yanzun Mafarautan ba su tuntubi hukumar yan sanda ba, kuma ba su mika wanda suka kama ba.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Masari ya maida zazzafan Martani ga kasurgumin dan bindiga, Bello Turji

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bayyana cewa babu maganar tsagaita wuta ko sulhu tsakanin gwamnati da yan bindiga

A martanin da ya yi wa wasikar Bello Turji, kasurgumin ɗan bindigan da ya addabi arewa, gwamnan yace baki ɗaya yan bindiga maƙaryata ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel