Wasikar Neman Sulhu: Gwamna Masari ya maida wa kasurgumin dan bindiga, Bello Turji Martani

Wasikar Neman Sulhu: Gwamna Masari ya maida wa kasurgumin dan bindiga, Bello Turji Martani

  • Gwamnan jihar Katsina ya yi fatali ta wasikar neman sulhu da Bello Turji ya aike wa gwamnati tarayya, yana bukatar tsagaita wuta
  • Aminu Masari yace lokacin sulhu ya wuce, kuma shi (Turji) bai isa ya kafa wa gwamnati wasu sharudda ba
  • Kasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi

Katsina - Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ya yi fatali da maganar zaman sulhu da yan bindigan, waɗan da suka addabi jiharsa da sauran jihohin arewa ta yamma.

Masari ya bayyana matsayarsa ne yayin zantawa da kafar watsa labarai ta DW hausa, ranar Asabar.

Premium times ta rahoto cewa gwamnan ya maida martani ga wasikar dake yawo ta neman zaman sulhu, wanda gawurtaccen ɗan bindiga. Bello Turji, ya aike wa gwamnati.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

Gwamna Masari
Wasikar Neman Sulhu: Gwamna Masari ya maida wa kasurgumin dan bindiga, Bello Turji Martani Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Waye shi da zai nemi a tsagaita wuta?

Gwamna Masari, wanda a baya gwamnatinsa ta rungumi tattaunawar sulhu, yace ba sauran tattaunawar sulhu tsakaninsu da yan bindiga.

Duk da babu adireshin sa a wasikar, Masari ya bayyana cewa abin da wasikar Turji ta ƙunsa ba gaskiya bane.

Gwamnan yace:

"Sulhu da wa? Waye shi da yake neman sulhu ko a tsagaita wuta? Shi babban maƙaryaci ne, bai isa ya faɗa mana yadda za'a zauna lafiya ko sulhu ba."
"Ƙaje ka samu iyalan waɗan da yan bindiga suka kashe, ku nemi sulhu da su, kuga yadda zata kaya. Kuma har da saka wasu sharuɗɗa, waye shi da zai kafa mana sharuɗɗa?"
"Shi ke neman sulhu amma har yana da bakin kafa wasu sharudda da za'a cika."

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

Tawagar Turji na ɗaya daga cikin kungiyoyin yan ta'adda da suka addabi yankin arewa maso yamma da wasu sassan arewa ta tsakiya.

Shin dagaske Turji ya nemi sulhu?

Legit.ng Hausa ta rahoto muku yadda Turji ya rubuta buɗaddiyar wasika zuwa ga shugaba Buhari, gwamna Matawalle na Zamfara, da sarkin Shinkafi, yana bukatar a tsagaita wuta a yi sulhu.

Wasu masana sun tabbatar da ingancin wasikar, wasu kuma sun yi zargin ya rubuta wasikar ne domin dakatar da luguden wutan jiragen yaki da kuma matsin lambar da sojojin ƙasa ke yi wa yan ta'addan.

A wani labarin kuma Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu.

A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Maganar sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje ta jawo ana ta ce-ce-ku-ce

Asali: Legit.ng

Online view pixel