'Karin bayani: 'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

'Karin bayani: 'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

  • Jami'an rundunar yan sanda sun kutsa cikin coci sun kama tsohon dan takarar gwamnan Imo a jam'iyyar AA a 2019, Uche Nwosu
  • Yanayin yadda jami'an tsaron suka afka coci suna harbe-harbe suka yi awon gaba da Nwosu a cikin mota yasa da farko mutane suke zargin masu garkuwa ne
  • Gwamman jihar Imo ta bakin kwamishinan watsa labarai na jihar Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnan na Imo ba shi da hannu cikin abin da ya faru

Imo - An shiga rudani a cocin St Peters da ke Eziama Obire a karamar hukumar Nkwere na jihar Omo, a ranar Lahadi, a lokacin da aka kama Uche Nwosu, surukin Sanata Rochas Okorocha.Yayin yadda aka kama shi ya janyo mutane suke tunanin kama sace Nwosu aka yi.

A wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, an ga mutane da bindiga suna awon gaba da Nwosu, a lokacin da ya hallarci addu'ar da ake yi bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Katafaren kantin 'Next Cash and Carry' da ke Abuja ya na ci da wuta

Yan sanda sun kama Nwosu, surukin tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha
Yan sanda sun kutsa coci sun kama Nwosu, surukin Rochas Okorocha. Hoto: The Nation
Asali: UGC

An ji muryar wasu mutane a bidiyon suna cewa 'An sace Nwosu'. An sace Ugwumba.'

Amma Daily Trust ta tabatar cewa kama Nwosu aka yi a safiyar ranar Lahadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da yan sanda suka ce

Mai magana da yawun yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abbatam ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa kama Nwosu aka yi.

Amma kuma bai bayyana dalilin da yasa aka kama shi ba.

Nwosu, wanda ya yi takarar gwamna a karkashin jam'iyyar Action Alliance, AA, a shekarar 2019, ya kuma rike mukamin shugaban fadar gwamna lokacin Rochas Okorocha na mulki.

An birne mahaifiyar Nwosu ne a karamar hukumar Eziama Obaire a karamar hukumar Nkwerre kwanaki hudu da suka gabata.

Babu hannun gwmanan Imo a kama Nwosu, Emelumba

Yayin da wasu daga cikin hadiman Nwosu suka yi ikirarin cewa an sace shi ne, wasu sun yi ikirarin cewa gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya sa aka kama shi.

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Amma, cikin wata sako da aka fitar cikin gaggawa, kwamishinan watsa labarai na jihar Imo, Declan Emelumba, ya ce gwamnan na Imo ba shi da hannu cikin abin da ya faru.

Ya ce 'rashin hankali' ne a yi ikirarin cewa gwamnan yana da hannu cikin bacewar Nwosu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel