Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF

Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF

  • Sadaukan sojojin saman Najeriya sun yi wa mayakan ISWAP luguden wuta inda suka halaka kwamandansu, Modu Kime, wanda aka fi sani da Abou Maryam
  • Ba kwamandan kadai aka halaka ba, wasu mayakan ta'addancin sun sheka lahira yayin da jiragen suka yi musu ruwan wuta a Bisko da Tumbum da ke yankin tafkin Chadi
  • Jami'in rundunar sojin ta tabbatar da cewa, sun dinga bibiyar inda kwamanda Abou Maryam ya ke da sharrikan da ya ke kullawa kafin su yi nasarar halaka shi

Borno - Dakarun sojin Najeriya sun halaka kwamandan kungiyar ta'addanci ta ISWAP, Modu Kime, wanda aka fi sani da Abou Maryam da mayakansa a wani luguden ruwan wuta da aka yi musu wuraren tafkin Chadi da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte

PRNigeria ta tattaro cewa, manyan kwamandojin kungiyar ta'addancin sun hadu da ajalinsu ne yayin da aka kai musu farmaki wuraren rafikan Bisko da Tumbum da ke karamar hukumar Abadam ta jihar.

An aiwatar da samamen ne bayan sintirin jiragen sama da kuma bayanan sirri da suka nuna cewa shugabannin ta'addancin suna wurin.

Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF
Nasrun Minallah: Kwamandan ISWAP, Abou Maryam, ya sheka barzahu sakamakon luguden sojin NAF. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Bayan kammala luguden daga jiragen yaki, an duba abinda ya faru a kasa inda aka tarar da 'yan ta'adda masu yawa da kwamandansu sun rasa rayukansu.

Wani jami'in sirri ya sanar da PRNigeria cewa, Abou Maryam, mai lambar waya +22788036182 an dinga bibiyar inda ya ke da kuma wadanda ya ke kira amma a sirrance.

"Na tsawon lokaci, mun dinga katse sadarwar shi da kuma yadda ya ke shirya ta'addanci a karkashin kungiyar wanda da yawa Borno ya ke shiryawa.

Kara karanta wannan

Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci

“Yana cin karensa babu babbaka a wuraren Tumbum Tawaye, Bisko, Garere, Arkumma da Dumbawa, Zari da Gundumbali.
“Abou Maryam ya shirya manyan farmaki kan sojojin Najeriya da wasu yankunan Damasak, Nganzai da Gajiram, a wasu lokutan kuwa har wajen Maiduguri."

Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin sama da ke yankin Ngomari a Maiduguri yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin sauka a birnin yau Alhamis.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, daya da cikin makaman masu linzami ya tsallake har zuwa Ajilari, kusa da filin jiragen sama na Maiduguri inda sansanin sojoji ya ke.

Majiyoyi sun ce mutum daya ya rasa ransa a Ngomari yayin da wasu suka samu raunika a yankin Ajilari. Alamu suna nuna cewa, maharan sun daidaita tare da saitar filin saukar jiragen saman ne saboda makaman sun sauka 10:45 na safe, mintoci kadan kafin isar Buhari birnin.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel