‘Yan Boko Haram sun hallaka mutane 5, raunata wasu a ranar da Buhari ya ziyarci Maiduguri

‘Yan Boko Haram sun hallaka mutane 5, raunata wasu a ranar da Buhari ya ziyarci Maiduguri

  • Ana tunanin mutane biyar sun mutu a harin da ‘Yan Boko Haram suka kai a safiyar ranar Alhamis
  • Sojojin Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād ake zargin sun tada bama-bamai a Maiduguri
  • Dakarun na ISWAP sun yi wannan danyen aiki ne a ranar da Muhammadu Buhari ya ziyarci Borno

Borno - Mutane akalla biyar aka tabbatar da cewa sun rasa ransu a harin da ‘Yan ta’addan Boko Haram suka kai a garin Maiduguri, jihar Borno.

Jaridar Punch ta fitar da karin bayani a ranar Juma’a, 24 ga watan Disamba, 2021, tace ana zargin mutane biyar sun rasu a sanadiyyar harin na jiya.

‘Yan ta’addan sun yi karfin hali sun harba wasu rokoki ne a daidai lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci garin Maiduguri.

Wata majiya a yankin Ajilari ta shaidawa manema labarai cewa bam din ya tarwatse a kusa da gidan wani Bawan Allah, har ya kashe budurwa.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Haka zalika an samu kananan yara biyu da bama-baman suka ji wa rauni a ranar Alhamis din. Zuwa yanzu ba a tabbatar da wanda ya kai harin ba.

Buhari
Buhari ya na jawabi a Maiduguri Hoto: @MuhammaduBuhari
Asali: Facebook

Sahara Reporters ta tabbatar da cewa dakarun na Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād ko ISWAP sun aika mutane biyar zuwa barzahu a jiyan.

Baya ga mace-macen da aka samu da kuma raunin da makaman suka ji wa wasu, ‘Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād sun jawo asarar dukiya.

Yankin Ngomari inda aka kai harin, kilomita kusan biyu ne da babban filin jirgin Maiduguri da sansanin sojojin sama, inda jirgin shugaba Buhari ya sauka.

Akwai wani bam da ya tashi a kusa da masallacin asibitin Umaru Shehu. Rahotannin sun ce hare-haren ba su yi wani illa baya ga wadannan wurare ba.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun fito da Malaman musuluncin da suka sace bayan an biya fiye da Naira miliyan 2

An yi dace a jawabinsa, Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ga bayan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

Buhari ya yi magana mai zafi

A Maiduguri ne aka ji shugaba Buhari yace gwamnatinsa ba zata sassautawa 'yan bindiga ba, har sai ta ga bayansu musamman a yankin Arewa maso yamma.

Shugaba Buhari yace idan 'yan Najeriya za su yi wa gwamnatinsa adalci, yanayin da ya samu kasar a 2015 da kuma halin da ake ciki a yanzun ba daya bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel