Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

  • An samu tashin hankali a yankin jihar Imo yayin da aka sace wani sarkin gargajiya da malamin fada a Owerri
  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun farmaki mai sarautar gargajiyar ne tare da yin awon gaba dashi
  • A halin da ake ciki ba a san inda 'yan bindigan suka yi ba, hakazalika, ba a samu jin ta bakin hukumar 'yan sanda ba

Owerri, jihar Imo - A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da babban limamin masarautar Owerri, Reginald Ejiogu, a karamar hukumar Owerri ta jihar Imo.

An yi garkuwa da Ejiogu ne tare da shugaban kauyen Umunwagbara na masarautar Owerri Nchi-Ise, Sunny Unachukwu.

Lamarin da wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro ya faru ne da yammacin ranar 18 ga watan Disamba, 2021.

Taswirar jihar Imo
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani ganau da ya so a sakaya sunansa, ya ce nan take aka yi awon gaba da wadanda abin ya shafa, aka tura su cikin mota, direban kuma ya tsere dasu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kasa samun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Mike Abattam domin jin ta bakinsa.

A baya-bayan nan ne ‘yan bindiga suka kai hari masarautun gargajiya a yankin gabashin kasar, musamman jihar Imo.

Hakan ya sa sarakunan jihar Imo suka fara buya bayan kashe-kashe da sace takwarorinsu da ake yi a jihar.

Kamar dai a kidayar baya, an kashe sarakunan gargajiya akalla biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama.

A cewar jaridar Leadership, ganau din ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Christ Church Road a Owerri, babban birnin jihar.

A kalamansa:

“Ba mu taba ganin irin wannan abu a baya ba. Wannan shi ne tozarta al'ada da al'adun mutanen Owerri..."

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Micheal Abattam, ya ce rundunar tana sa ido kan lamarin kuma za ta shaidawa manema labarai abubuwan da ake ciki.

Gwamnan APC ya gano masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa, ya saka ranar fallasa su

A baya kadan, Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin bayyana sunayen wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a jihar Imo da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da za a gudanar a ranar Litinin 3 ga watan Janairu, 2022.

Ya yi bayanin cewa wasu mutane 18 ne da jami’an tsaro suka kama kwanan nan kan kashe kansiloli biyu a jihar, sun bayyana sunayen wadanda suke haddasa rashin tsaro, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel