Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

  • Miyagun 'yan ta'adda sun afka wa jerin gwanon motoccin 'yan kasuwa da sauran matafiya a hanyar Kaduna - Birnin Gwari a hanyarsu ta zuwa Kano
  • Wani shugaban al'umma, Muhammadu Umaru ya bayyana cewa lamarin ya ritsa da makwabtansu hudu da motar yan sanda da ta yi musu rakiya
  • ASP, Jalige Mohammed, mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna, ya yi alkwarin zai yi tsokaci kan lamarin bayan ya samu cikakken bayani game da lamarin

Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun sace matafiya da dama a kan hanyar Kaduna - Birnin Gwari a ranar Laraba bayan kai musu hari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan harin da aka kai misalin karfe 11 amma an gano cewa mafi yawancin wadanda abin ya faru da su yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto wasu mutane da aka sace, sun yi ram da masu satar shanu

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari
'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wani shugaban al'umma, Muhammadu Umaru, ya shaida wa Daily Trust cewa hudu daga cikin makwabtansa suna daga cikin wadanda aka sace, ya kara da cewa yan sanda sun yi wa motoccin da suka kai 20 rakiya.

Ya ce:

"Akwai 'yan kasuwan mu kimanin 70 daga Udawa kuma akwai wasu daga garuruwan da ke makwabtaka da mu a cikin jerin gwanon motoccin a tsakanin Udawa zuwa Buruku a kan babban titin.
"Abin ya ritsa da makwabta na saboda mun kira wayansu amma 'yan bindiga ne suka dauka."

An gano cewa wasu daga cikin yan kasuwan sun tsere cikin daji sannan suka kira yan uwansu suka sanar da su abin da ya faru.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Kaduna, ASP, Jalige Mohammed, ya yi alkwarin zai yi tsokaci kan lamarin bayan ya samu cikaken bayani.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Kaduna: Sarkin Zazzau Ya Bukaci Limamai Da Fastoci Su Fara Addu’o’i Na Musaman Kan 'Yan Bindiga

A wani rahoton, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi kira ga dukkan limamai da fastoci da ke masarautar Zazzau su fara addu'a na musamman don ganin an samu zaman lafiya a yankin da ma kasa baki daya, Daily Trust ta ruwaito.

Bamalli, wanda ya bayyana hakan cikin takardar da mai magana da yawun masarautar, Malam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar ya ce hakan ya zama dole ne saboda yawai kashe-kashe da hari da garkuwa da mutane da ake yi a masarautar.

Ya bukaci dukkan musulmi su fara yin addu'o'in na musamman a salloli biyar na kowanne rana yayin da kiristoci kuma a yayin addu'o'in su na coci don neman Allah ya kawo sauki, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel