Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?

Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?

Wasu hotuna suna ta yawo wadanda ake cewa na jama'ar da farmakin 'yan bindiga na jihar Sokoto ya ritsa da su ne. Yankin arewa maso yamma ya na fuskantar jerin farmakin 'yan bindiga, lamarin da ya lamushe rayukan jama'a masu tarin yawa.

A ranar 6 ga watan Disamba, fasinjoji 23 'yan bindiga suka babbaka a wata mota a jihar Sokoto. Bayan kwanaki kadan, 'yan bindigan sun sake komawa kauyen inda suka sace mutane tare da kashe wasu biyun.

Hotunan da ake ta wallafawa a Twitter da Facebook sun nuna gawawwakin Musulmai a jere ana yi musu jana'iza yayin da wani kuma ke nuna konannen wurin.

Wata ma'abociyar amfani da Twitter mai suna @DrHalimah mai mabiya 1,926, ta wallafa hotunan a ranar 10 ga watan Disamba inda ta yi tsokaci da:

Kara karanta wannan

Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

"Kashe-kashen 'yan bindiga na Sokoto. Idan kai Muslumi ne kuma kana nan, don Allah ka yada albarkacin Juma'ar nan".
Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?
Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?. Hoto daga @DrHalima
Asali: Twitter

Wannan wallafa kuwa an sake wallafa ta ya kai sau 1,000 kuma an jinjina mata ya kai 800.

Wata ma'abociyar amfani da Facebook mai suna Hyshat Haruna, ta wallafa hotunan tare da yin tsokaci kamar haka:

"Kashe-kashen Sokoto wanda 'yan bindiga suka yi, idan kai Musulmi ne kuma kana nan, don Allah ka yada wannan.

Amma da gaske wadannan sabbin hotuna ne?

Domin tabbatar da ingancin wallafarsu, TheCable ta dubo hotunan inda ta hango ire-irensu da yawa a google.

Hoto na farko

Hoton ya bayyana a Vanguard Newspaper. A labarin da aka wallafa tun 2019 inda hoton ke dauke da tsokacinsa "kashe-kashen Zamfara".

Kara karanta wannan

Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?
Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?. Hoto daga Vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Hoto na biyu

BBC Pidgin ce ta wallafa hoton a Mayun 2020 inda ta bayyana shi da kashe-kashen Zamfara kuma ta hada shi da rahoton kashe wasu mazauna karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?
Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?. Hoto daga bbc.com
Asali: UGC

Hoto na uku

Hoton na uku wanda ke kunshe da gawawwaki 36 ana yi musu jana'iza, ya nuna cewa hotunan wasu mutane ne da 'yan bindiga suka kashe a kauyen Birane da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara a watan Fabrairu 2018.

Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?
Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hoto na hudu

Hoto na hudu kuwa, ya na kunshe ne da manoman shinkafa 43 wadanda 'yan ta'addan Boko Haram suka kashe a kauyen Zabarmari na karamar hukumar Jere a jihar Borno a 2020.

Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?
Bincike: Mene ne gaskiya kan hotunan gawawwakin da ke yawo da sunan na Sakwatawa ne?. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hukunci

Bincike ya nuna cewa, hotunan da suka karade shafukan sada zumuntar zamani ba su da alaka da babbaka mutane da 'yan bindiga suka yi a Sokoto.

Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci

Kara karanta wannan

Da duminsa: Boko Haram sun kai sabon farmaki Borno, sun kone gidajen jama'a

A wani labari na daban, kungiyar hadin kan Arewa, ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa akan nuna tausayi ga wadanda ta’addanci ya shafi yankinsu.

TheCable ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Litinin wacce Emmanuel Yawe, Sakataren watsa labaran kungiyar ACF ya saki, ya yi alawadai da kisan mutane 38 na karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Kungiyar ta bukaci Buhari, gwamnoni da sauran shugabannin arewa da su yi iyakar kokarinsu wurin nuna kula ga wadanda lamarin ya ritsa da su, Daily Trust ta ruwaito haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel