Matasan Arewa sun tura sako ga gwamnatin Buhari kan lamarin 'yan bindiga

Matasan Arewa sun tura sako ga gwamnatin Buhari kan lamarin 'yan bindiga

  • Mtasa a Arewacin Najeriya sun mika sakon su ga gwamnatin Buhari, sun ce ya kamata gwamnati ta duba lamarin tsaro
  • Matasan sun nemi gwamnati ta gaggauta daukar mataki wajen dakile 'yan ta'adda a yankin Arewacin kasar
  • A yau ne 'yan wata kungiya a Arewacin Najeriya suka gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Zariya ta jihar Kaduna

Kaduna - Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ba da umarni ga rundunar tsaro ta musamman a Arewacin kasar domin fatattakar ‘yan ta’adda da kuma ruguza su a yankunan Arewacin kasar nan.

Matasan da suka gudanar da zanga-zangar lumana a garin Zariya ta jihar Kaduna, domin nuna adawa da kashe-kashe da sace-sacen jama’a da ake yi domin neman kudin fansa da ’yan ta’adda ke yi, sun neki a gagauta daukar matakin tarwatsa 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

Taswirar jihar Kaduna
Matasan Arewa sun tura sako ga gwamnatin Buhari kan lamarin 'yan bindiga | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mmasu zanga-zangar sun kuma nuna damuwarsu kan sace mutane da ya afku a babbar hanyar Zariya zuwa Kaduna, wanda suka bayyana a matsayin wata babbar hanyar shiga jihohin Arewa da dama amma yanzu ta zama tarkon mutuwa ga matafiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun yi dandazo a kan gadar Kwangila da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, sun yi tattaki zuwa yankin PZ da ke karamar Hukumar Sabon Gari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce an gansu dauke da kwalaye da rubutu kamar haka: “Zaria peace walk against insecurity, “End insecurity now, “North is bleeding” da kuma “secure north.”

Da yake jawabi ga manema labarai a yayin zanga-zangar, mataimakin kodinetan kungiyar na shiyyar Arewa maso yamma, Kwamared Sani Sa’ed Al-Tukry, ya ce dole ne a kawar da wadanda ke dagula yankin Arewa ko kuma a kama su domin su fuskanci fushin doka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Kamar yadda Pulse ta tattaro, AlTukry ya bayyana da cewa abin takaici ne kusan kullum ana garkuwa da jama'ar da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai cewa:

“Wannan labari ne na jini da hawaye da cizon hakora wanda bai kamata a ci gaba da yi ba."

Ya ce daukacin yankin Arewa na zubar jini, kuma babu inda ake zaune akalau, inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta umarci jami’an tsaro su tashi tsaye kan lamarin.

Ya kuma nemi gwamnati ta sa jami'an tsaro su ci gaba da gudanar da ayyukansu musamman a hanyoyin Zaria-Kaduna, Kaduna-Abuja, Kaduna-Birnin Gwari-Neja, Birnin Gwari-Titin Funtua-Katsina-Zamfara-Sokoto.

A cewar Al-Tukry:

“Arewa a yau kamar jirgin ruwa ne da ke nutsewa kuma ke shirin kifewa, akwai bukatar a tsaya tsayin daka bisa wata maslaha ta kasa da aka amince da ita ba tare da la’akari da siyasa, addini da kabilanci ba.
"Ya kamata tsarin tsaron kasa ya inganta damar da Najeriya ke da shi na dakile tashe-tashen hankula ko ta'addanci a fadin kasar ta yadda tare, za mu hada karfi da karfe don gina kasar da za a zauna lafiya da adalci."

Kara karanta wannan

Kungiya Ta Yi Kira Ga 'Yan Kudancin Najeriya Su Saka Baki Don Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe a Arewa

Mata masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa 'yan bindiga

A wani labarin, wasu mata biyu masu juna biyu a jihar Neja sun haihu a kan wani tsauni a lokacin da suke kokarin tserewa hare-haren ‘yan bindiga a yankinsu.

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa harin da aka kai a kauyen Kwimo da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja ya sa daukacin al’ummar yankin tserewa don tsira da rayukansu.

A cewar wani ganau mai suna Usman Kwimo, ba zai iya tabbatar da halin lafiyar mata masu juna biyun da jariransu ba saboda ba su da kayan aikin jinya da ake bukata don kula da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel