Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci

Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci

  • Kungiyar ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa akan nuna wa yankunan da ta’addanci ya rutsa da su tausayi
  • Sakataren watsa labaran kungiyar, Emmanuel Yawe, ya sanar da hakan ta wata takarda ta ranar Litinin inda ya yi alawadai da kisan mutane 38 na jihar Kaduna
  • Kungiyar ta bukaci shugaban kasa, gwamnoni da sauran manyan shugabannin arewa da su yi iyakar kokarinsu wurin nuna kulawa da tausayi ga wadanda lamarin ya ritsa da yankinsu

Arewa - Kungiyar hadin kan Arewa, ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa akan nuna tausayi ga wadanda ta’addanci ya shafi yankinsu.

TheCable ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Litinin wacce Emmanuel Yawe, Sakataren watsa labaran kungiyar ACF ya saki, ya yi alawadai da kisan mutane 38 na karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci
Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kungiyar ta bukaci Buhari, gwamnoni da sauran shugabannin arewa da su yi iyakar kokarinsu wurin nuna kula ga wadanda lamarin ya ritsa da su, Daily Trust ta ruwaito haka.

“ACF ta nuna rashin amincewar ta, rashin yardar ta da fushin ta akan kisan da ya ki ci ya ki cinyewa a arewacin Najeriya,” Kamar yadda takardar ta zo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Lamarin da ya auku a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda aka halaka rayuka 38 wadanda ba su ji ba basu gani ba.
“Kamar yadda Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya shaida, an lalata gidaje, motoci da hatsi da dama sakamakon harin.
“Yayin da ACF ta ke taya gwamnan jihar Kaduna da shugaban kasar Najeriya tausar wadanda asara ta afka musu sakamakon harin, muna kira ga gwamnatin jihohi da ta tarayya da su nuna tausayi da jin kai ga wadanda rashin tsaro ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

“Babu abinda ya hana shugaban kasa da gwamnonin jihohi kai ziyara wurare. Cikin takaici mun lura da yadda bai nuna dacewar yin hakan ba, misali babu wani gwamna da ya ke zuwa jaje banda gwamna Zulum na jihar Borno. Ba a dade ba da aka halaka mutane 10 a Uba-Askira a Borno, sannan an sace wasu da dama.
“Shugaban kasa da gwamnonin arewa su na ta nuna cewa rayukansu da na iyalansu su ne kadai masu muhimmanci.
“ACF ta yarda da cewa shugaban kasa da gwamnonin arewa su na da damar yin fiye da hakan," takardar ta kara da cewa.

Kisan Kaduna: Ku karar min da ragowar 'yan ta'adda, Buhari ga hukumomin tsaro

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da hare-haren kwanan nan da 'yan bindiga ke kai wa Kaduna, inda ya kwatanta su da 'yan ta'adda.

Rayuka talatin da takwas aka tabbatar da mutuwarsu bayan farmakin da 'yan bindiga suka kai wasu yankuna da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

Wannan lamarin na zuwa ne bayan kwanaki kadan da kotu ta ayyana kungiyoyin 'yan bindigan da 'yan ta'adda.

A wata takarda da Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Buhari ya ce maharan suna "jin radadin zafin" ayyukan cikin kwanakin nan da jami'an tsaro ke yi, hakan yasa suke kai wa yankuna farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel