Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa da amince da naɗin sabon Minista, Muazu Sambo

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa da amince da naɗin sabon Minista, Muazu Sambo

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Mu'azu Sambo a matsayin ministan wutar lantarki a Najeriya bayan shafe lokaci tana tantance shi
  • Sambo, wanda ya fito daga jihar Taraba, ya sha alwashin aiki tukuru wajen tabbatar da an kammala aikin tashar wutan Mambila
  • A cewarsa cikin shekara ɗaya za'a ga canji, domin ya san matsalar da hanyar warware ta tun kafin ya shiga ofis

Abuja - Majalisar dattawan tarayyan Najeriya ta tabbatar da Mu'azu Sambo, a matsayin sabon minista Lantarkia Najeriya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Babbar majalisar ta amince da naɗinsa ne bayan kwashe fiye awa ɗaya tana tantance shi ranar Talata 21 ga watan Disamba.

Ana tsammanin za'a rantsar da Sambo a matsayin sabon minista biyo bayan tabbatar da shi da majalisar dattawa ta yi.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai kare ka: Na san matsalar Mambilla, a ba ni shekara 1 a ga canji inji Sabon Minista

Mu'azu Sambo
Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa da amince da naɗin sabon Minista, Muazu Sambo Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Zan warware matsalolin aikin Mambila

Yayin da sanatocin ke tantance shi, Sambo ya sha alwashin bankado duk wasu abubuwan dake zama cikas ga aikin tashar samar da wutar lantarkin Mambila.

Yace akwai hanyoyin da za'a bi a shawo kan kamfanin samar da wutar lantarki daga hasken rana Sunrise Power Transmission Company of Nigeria Ltd (SPTCL).

Kamfanin dai ya garzaya ya maka Najeriya a kotun sulhu dake Farisa, kasar Faransa yana neman a biya shi diyya bisa warware yarjejeniya.

Ya nemi gwamnatin Najeriya ta lale masa dala biliyan $2,354bn a matsayin diyya bisa warware yarjejeniyar 2003 na gina tashar lantarki da zata samar da 3,050MW a Mambila, jihar Taraba.

Meyasa aikin Mambila ke kwan gaba kwan baya?

Sambo ya bayyana cewa abin da takaici bayan kwashe shekaru da ambaton fara aikin tashar wutan amma har yanzun ba'a kammala ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari da Uwargidarsa sun dawo gida Najeriya

Premium Times ta rahoto Sambo yace:

"Wannan wani aiki ne da aka fara tun a jamhuriya ta farko, amma har yanzun sai dai zance amma an ƙi kammala shi."
"Nasan cewa abinda ya hana aikin cigaba yana da alaƙa da shari'ar da aka shigar a Faris. Akwai hanyar da zamu sasanta da kamfanin da ya kai mu gaban kotu."
"Zan tabbatar da yin wani abu kan lamarin cikin shekara ɗaya. Nasan inda matsalar take kuma nasan hanyar magance ta."

A wani labarin kuma Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu sai baba ta gani

Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari , ta umarci baki ɗaya ma'aikatan ofishinta su tafi hutu har sai sun ji daga gare ta.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke yaɗa jita-jitar cewa ko matar shugaban tana da juna biyu ne.

Kara karanta wannan

Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas

Asali: Legit.ng

Online view pixel