Da Dumi-Dumi: Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu

Da Dumi-Dumi: Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu

  • Mai dakin shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta baiwa ma'aikatan ofishinta hutu har sai baba ta gani
  • Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke yaɗa jita-jitar cewa ko matar shugaban tana da juna biyu ne
  • Sai dai hadimin Aisha Buhari, Sulaiman Haruna, ya musanta rahoton, inda yace shugabarsa na cikin koshin lafiya

Abuja - Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta umarci baki ɗaya ma'aikatan ofishinta su tafi hutu har sai sun ji daga gare ta.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da uwar gidan shugaban ta fitar a shafinta na dandanlin sada zumunta Instagram (@aishambuhari).

Sanarwan na ɗauke da sa hannun babban mai baiwa shugaba Buhari Shawara kan harkokin lafiya, Dakta Mohammed Kamal, da haɗin guiwar ofishin matar shugaban ƙasa.

Aisha Buhari
Da Dumi-Dumi: Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sanarwan ta ƙara da cewa ayyukan ofishin zai cigaba da gudana ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually).

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan Majalisar Wakilai sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn

Sanarwan tace:

"Muna sanarwa ma'aikata cewa za'a rufe ofishin uwar gidan shugaban ƙasa saboda matsowar lokacin bukukuwan kirsimeti da kuma sabuwar shekara."
"Saboda haka a yanzun, ana umartan dukkan ma'aikatan ofishin su tafi hutu sai sanda suka ji sanarwa ta gaba."
"Sai dai ku sani za'a cigaba da gudanar ayyukan ofishin daga gida ta hanyar amfani da fasahar zamani wato Virtually."

Daga nan sai uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta mika godiyarta ga ma'aikatan bisa sadaukarwan su da jajircewa, kuma ta musu yin fatan shagulgula lami lafiya.

Shin dagaske tana da ciki?

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da mutane ke ta yaɗa hotunanta, suna cewa da yuwuwar matar shugaban ta yi nauyi ne.

Sai dai hadimin Aisha Buhari, Sulaiman Haruna, ya musanta jita-jitar dake cewa uwar gidansa na ɗauke da juna biyu.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan sabon kundin zabe 2021 da Buhari ya ki sa hannu

Ya kuma tabbatar da cewa matar shugaban ƙasa tana cikin koshin lafiya 100% kuma ba ta ɗauke da ciki kamar yadda ake yaɗawa.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan zuwansa Legas da rashin zuwa jaje Sokoto

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kare kansa daga sukar da yake sha bayan zuwa Legas a lokacin da aka kashe mutane a Sokoto.

Malam Garba Shehu, yace ba kaddamar da littafi ya kai Buhari Legas ba, ainihin makasudin zuwansa dan jiragen ruwan sojoji ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel