Aiki ga mai kare ka: Na san matsalar Mambilla, a ba ni shekara 1 a ga canji inji Sabon Minista

Aiki ga mai kare ka: Na san matsalar Mambilla, a ba ni shekara 1 a ga canji inji Sabon Minista

Sabon Ministan harkar wutar lantarki yace a cikin shekara guda za a ga canji a tashar wutar Mambilla

Muazu Sambo ya bayyana wannan ne a lokacin da ake tantance shi a majalisar dattawan Najeriya

Sambo ya fadawa Sanatoci cewa ya san inda matsalolin su ke, yace shawo kan su ba zai gagare shi ba

Abuja - Muazu Sambo, sabon Ministan harkar wutar lantarki a Najeriya, ya yi alkawarin kawo karshen matsalar da suka hana tashar Mambilla aiki.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Muazu Sambo ya yi wannan alwashi ne da ya bayyana a gaban Sanatoci a majalisar dattawan Najeriya a dazu.

Da ‘yan majalisa su ke yi masa tambaya yayin da aka tantance shi a ranar Talata, 21 ga watan Disamba, 2021 an bijiro masa da batun aikin Mambilla.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Muazu Sambo yace jinkirin da aka samu wajen wannan gagarumin aiki abin takaici ne sosai.

Sabon Minista
Muazu Sambo Hoto; www.thecable.ng
Asali: UGC

Abin da Sambo ya fadawa Sanatoci

“Ina tare da ku a kan batun rashin cigaban da aka samu a aikin Mambilla. Tun jamhuriya ta farko ake abu daya, idan a 2021 ba a fara aikin ba, abin takaici ne.”
“Babban kalubalen da ake samu shi ne shari’ar da ake yi a Faris. Dole a nemi yadda za a sasanta da kamfanin da suka kai mu (gwamnatin Najeriya) kotu.”
“Idan aka tabbatar da ni a majalisar dattawar nan, labarin aikin Mambilla zai canza a cikin shekara guda. Na san inda matsalar take, kuma zan magance ta.”
“Matsalar nan ta harka da mutane ce. A shekaru 35 da suka wuce, na yi aikin biliyoyin daloli. Saboda haka ba sabon abu ba ne ni a wuri na.” – Muazu Sambo.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

Abin da ya jawo gine-gine suke fadi

Haka zalika Mu’azu Sambo ya yi magana game da yadda gine-gine suke rushewa a kasar nan.

Daga cikin dalilan da ya bada akwai amfani da kayan aiki marasa kyau, dauko bara-gurbin ma’aikata, rashin dokoki da kin yin gwajin kasa kafin a fara gini.

Rahoton yace Sanatoci irinsu Shuaibu Lau (APC, Taraba), Orji Kalu (APC, Abia) da kuma Yusuf Yusuf (APC, Taraba), sun gamsu da bayanan da Sambo ya yi masu.

Littafin da Bisi Akande ya rubuta

An ji cewa daya daga cikin manyan abokan gaban Bola Tinubu, watai Bode George ya yi kaca-kaca da littafin 'My Participation' da Cif Bisi Akande ya rubuta

George yace da biyu aka rubuta wannan littafin, domin kurum Bola Tinubu ya yi kasuwa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel