Kano: Awanni bayan yankewa wasu hukunci a kotu, an sake kama wani matashi da katin ATM 576 a filin jirgin sama

Kano: Awanni bayan yankewa wasu hukunci a kotu, an sake kama wani matashi da katin ATM 576 a filin jirgin sama

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta bayyana yadda ta kama wani mutum bayan bai wuci sa’o’i biyu da kama wani na daban ba da katinan banki guda 1,144 a filin jirgi
  • A ranar Talata Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya saki wata takarda wacce ya ce a ranar Litinin jami’an hukumar da hadin kan jami’an filin jirgin sama su ka kama Khalil Bashir Lawal
  • An kama Lawal wanda ya ke yunkurin wucewa Uganda ta jirgin Ethiopian da katina 576 da katinan banki masu sunaye mabanbanta wadanda ya adana a cikin kayansa

Jihar Kano - Hukumar yaki da rashawa da masu yiwa arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta ce ta kama wani mutum a filin jirgin Malam Aminu Kano, da katinan banki guda 576, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

Hukumar ta bayyana hakan ne ta wata takarda wacce kakakinta, Wilson Uwujaren, ya saki a ranar Talata, inda ta ce sun kama wani bayan sa’o’i biyu da kama wani mutum na daban da katinan banki a 1,144 a filin jirgin.

EFCC ta sake kama wani mutum da katin ATM 576 a Jihar Kano
Kano: EFCC ta sake kama wani matashi da katin ATM 576 a filin jirgin sama. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Uwujaren ya ce jami’an filin jirgin da jami’an hukumar kwastom sun hada kai wurin kama wanda ake zargin, Khalil Bashir Lawal, a ranar Litinin, 20 ga watan Disamban 2021.

Ya na yunkurin wucewa Uganda ta jirgin Ethiopia ne

Bayan kama shi, an gano cewa Lawal ya na son wucewa Uganda ne ta jirgin Ethiopian, kuma ya adana katinan banki guda 576 na mutane da bankuna daban-daban a cikin kayanshi.

Da aka kammala binciken an gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu, kamar yadda takardar EFCC ta shaida.

Wanda aka kama da farko kamar yadda Mr Uwujaren ya shaida a wata takarda, ya na kokarin sumogal din katinan banki 1,144 zuwa kasar waje.

Kara karanta wannan

Kwastam ta samu kudin da suka zarce abin da aka daurawa Hameed Ali ya yi a shekarar nan

A cewarsa kamar yadda Premium Times ta rahoto, mutane ukun da ake zargi, Abdullahi Usman, Musa Abubakar da Abdulwahid Auwalu su na hannun hukumar EFCC bayan kama su a lokuta daban-daban, tsakanin ranar 24 ga watan Nuwamba zuwa ranar 1 ga watan Disamban 2021.

Duk sun amsa laifukansu

An gano cewa Musa Abubakar ya na yunkurin wucewa Dubai ne, daukar larabawa (UAE), inda ya adana katinan banki guda 714, yayin da aka kama Abdullahi Usman shi kuma zai wuce Saudi Arabia da katina 298.

Abdulwahid a dayan bangarensa shi kuma an kama shi da katinan banki guda 132 yana kokarin wucewa Istanbul, kasar Turkiyya ta jirgin Ethiopia.

Duk wadanda aka kama sun amsa laifuka guda uku da ake zarginsu.

Tuni kotu ta yanke musu hukunci

Alkalin kotun, Tanimu Shehu na babbar kotun Kano a ranar Litinin ya yanke wa wadana aka kama hukuncin watanni shida a gidan gyaran hali ko kuma su biya tarar N50,000.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

A wani labarin, Hukuma EFCC, ta gurfanar da wani Ishaq Abubakar gaban Mai Shari'a P.Lifu na Kotu Trayya da ke zamanta a Ikoyi, kan laifuka 11 da suka shafi intanet.

The Punch ta rahoto cewa jami'an Kwastam ne suka kama wanda ake zargin a ranar 22 ga watan Agustan 2020, a filin tashin jirage na Murtala Mohammed, Legas yana hanyar zuwa Dubai da katin ATM 2.863 da katin waya hudu a cikin kwalin Indomie.

Mataimakin kwantrola na Kwastam, Abdulmumin Bako ya mika shi ga Hukumar EFCC a ranar 10 ga watan Satumban 2020, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel