Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Bayan Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja

Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Bayan Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja

  • Mazauna garin Rafindaji da ke yankin Gulida a Abaji da ke cikin Abuja sun shiga cikin tashin hankali bayan ‘yan bindiga sun fatattaki manoma daga gonakinsu tare da garkuwa da mutane biyu
  • Wani mazaunin yankin, Dalami Ishaku ya sanar da manema labarai hakan inda ya ce sun sace wasu manoma biyu ‘yan kabilar Tibi mazauna Rafindaji su na hanyar komawa gida a babur
  • Dagacin kauyen Gulida, Sardauna Abubakar, ya shaida yadda ya je kai wa shugaban karamar hukumar rahoto akan sace mutane biyun inda ya ji batun korar wasu manoman daga gonakinsu

Abuja - Mazauna Rafindaji a kauyen Gulida da ke cikin Abaji a FCT sun shiga tashin hankali bayan sun samu labarin yadda ‘yan bindiga su ka fatattaki manoma a gonakinsu tare da yin garkuwa da mutane biyu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Mazaunin yankin, Danlami Ishaku, yayin tattaunawa da City News ya bayar da sunayen wadanda su ka sace inda ya ce akwai Ezikel Tsenongu da Clement Ubun, wadanda a cewarsa manoma ne na kabilar Tibi kuma su na makwabtaka da garin Rafindaji ne.

Jama’a Sun Shiga Tashin Hankali Bayan Ƴan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja
'Yan Bindiga Sun Fatattaki Manoma Daga Gonakinsu, Sun Kuma Sace 2 a Abuja. Hoto: Daily Trust/Bulama
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa an yi garkuwa da mutane biyun ne a ranar Lahadi da misalin karfe 4:34 na yamma yayin dawowa daga kauyen Madani da ke kusa da su a babur inda su ka je gaishe da abokan arzikinsu.

Ya ce su na babur masu garkuwa da mutanen su ka tasa keyarsu

Kamar yadda ya shaida:

“Wasu manoma biyu su na hanyar dawowa daga kauyen Madani su ka ci karo da wasu ‘yan bindiga rike da miyagun makamai, take a nan su ka yi awon gaba da su.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

A cewarsa ‘yan bindigan sun je da yawansu har garin Gulida a ranar Litinin da safe inda su ka fatattaki manoma su na tsaka da ayyuka a gonakinsu.

Dagacin kauyen Gulida ya tabbatar da satar mutanen

Dagacin kauyen Gulida, Sardauna Abubakar, yayin tattaunawa da wakilin Daily Trust, ya tabbatar da satar manoman guda biyu da ‘yan bindiga su ka yi.

Ya shaida cewa:

“Ina Abaji tare da wasu fadawa na, inda na je sanar da shugaban karamar hukumarmu batun yadda wasu ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da jama’a, sai ga wani ya zo da batun yadda su ka fatattaki wasu manoma daga gonakinsu.”

A cewarsa har ya sanar da shugabannin karamar hukumar halin da ake ciki na rashin tsaron.

Bayan tuntunar kakakin rundunar ‘yan sandan FCT magana, DSP Adeh Josephine, ya ce ba a kai musu rahoto akan lamarin ba.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel