Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

  • Sojojin Najeriya sun dura daji, sun fatattaki wasu 'yan bindiga da dama da aka ce masu biyayya ga Bello Turji ne
  • A halin da ake ciki, sojojin sun ce ba zasu fito daga dajin ba har sai sun yi raga-raga da mafakar 'yan bindiga
  • A baya dai an samu afkuwar wani mummunan hari a Sokoto, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da dama

Sokoto - An kashe ‘yan bindiga da dama yayin wani artabu da sojoji a kauyen Katanga da ke karamar hukumar Isa a jihar Sokoto a ranar Alhamis.

Daily Trust ta tattaro cewa kauyen na karkashin ikon ‘yan bindiga ne kafin a yi arangamar.

Wani mazaunin garin ya shaida cewa Katanga da Satiru har yanzu suna karkashin ikon ‘yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa

Taswirar jihar Sokoto
Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani dan banga, wanda ke cikin wadanda suka fatattaki'yan bindigan, ya ce rundunar ta samu jagorancin babban kwamandan shiyya ta 8 na rundunar sojojin Najeriya, kuma tawagar ta kunshi wasu manyan hafsoshi ciki har da kwamandan Garrison na sashin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Sama da motoci 20 ne suka afka wa yankin, mun yi ta fafatawa da su na tsawon sa’o’i da dama, hasali ma sai da jiragen yaki suka zo suka tilasta musu ja da baya suka kuma yi kasa a gwiwa.
“Yayi wuri in bayyana adadin ‘yan ta’addan da aka kashe a yayin arangamar, amma babu ko daya da ya jikkata a bangarenmu. Don haka aikin ya samu nasara."

Wani mazaunin garin Isa, ya shaida cewa, an ga ‘yan bindiga da dama sun nufi yankin domin tallafa wa mutanensu a yayin arangamar.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

“Amma daga bayanan da suke zuwa mana, sojoji sun yi musu raga-raga.
"Kamar yadda nake magana da ku, GOC da mutanensa suna ci gaba da kutsawa kurmin danin don neman mafakar 'yan bindigan."

A cewar wata majiyar soji, GOC ta sha alwashin ba za ta dawo ba har sai sun kawar da dukkan matsugunan 'yan bindiga da ke gabashin Sakkwato.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta raba kayan agaji ga wadanda ‘yan bindigan suka yiwa barna a jihar.

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Wasu daga cikin yan bindigan da suka kashe masallata 18 a kauyen Maza-Kuka, karamar hukumar Mashegu, jihar Neja, sun shiga hannu.

Kwamishinan kananan hukumomi, cigaban karkara, harkokin nade-nade da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, shi ne ya sanar da haka yayin da yake bayani ga manema labarai a Minna ranar Laraba.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan na cewa ba zai iya bayyana adadin waɗan da suka shiga hannu ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka, an sace wasu yayin da ‘Yan bindiga suka yi ta’adi a titin Zaria-Kaduna

'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa

A wani labarin, Daily Trust ta rahoto cewa, wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari, inda suka kashe wani Alhaji Habibu na yankin Sayen Lenu a Dutsen Abba na karamar hukumar Zariya a Kaduna tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa uku.

Sayen lemu wani kauye ne da ke kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya, kuma yana da tazarar kilomita 5 daga inda ‘yan bindiga suka tare hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Litinin.

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun isa gidansa da misalin karfe 11 na daren Laraba inda suka harbe shi har lahira sannan suka yi awon gaba da ‘ya’yansa uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel