'Yan daba sun zagaye OAU, sun kai wa shugaban jami'a da ma'aikata farmaki

'Yan daba sun zagaye OAU, sun kai wa shugaban jami'a da ma'aikata farmaki

  • Wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne a ranar Litinin sun kai farmaki jami’ar Obafemi Awolowo a Ile-Ife inda su ka kai wa shugaban jami’ar, Farfesa Eyitope Ogunbodede hari
  • Ba a kansa kadai su ka tsaya ba, dama sun isa da miyagun makamai kamar bindigogi da adduna inda su ka dakatar da shugaban makarantar da jama’arsa da dama
  • Sun dinga harbe-harbe ko ta ina kuma ana zargin masu kwacen filaye ne su ka tura matasan don son su kwace wani filin makarantar da karfi da yaji

Ile-Ife, Osun - Wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki wani bangare da ke cikin jami’ar Obafemi Awolowo a Ile-Ife inda su ka kai wa shugaban jami’ar hari, Farfesa Eyitope Ogunbodede da wasu ma’aikatan jami’ar.

Matasan rike da miyagun makamai ciki har da masu bindigogi da adduna, sun dakatar da shugaban makarantar da wasu jami’ansa yayin da su ke kokarin kwace wani bangare daga jami’ar tare da harbe-harbe ko ta ina, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

'Yan daba sun zagaye OAU, sun kai shugaban jami'ar farmaki
'Yan daba sun zagaye OAU, sun kai shugaban jami'ar farmaki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

‘Yan daban sun kai wa jami’in hulda da jama’an jami’ar, Mr Abiodun Olanrewaju farmaki, tare da manema labarai inda su ka yi yunkurin halaka su.

Ana zargin masu kwacen filaye ne su ka yi hayarsu don kwace wani bangare na jami’ar, Daily Trust ta ruwaito.

Ogunmodede ya kwatanta harin a matsayin mummunan lamari inda ya ce gwamnatin tarayya ba za ta gushe ba har sai ta kare filin jami’ar.

Bai dade da kammala dakin kwanan dalibai ba inda masu kwacen filayen su ke yunkurin kwacewa saboda kokarin zama cikas ga rayuwar dalibai.

Shugaban Jami’ar ya ce:

“Bana son in yi asarar ran kowanne dalibinmu.
“Ba mu da wuraren kwana isassu don dalibai amma hakan ba ya nufin za mu sadaukar da rayuwar wani dalibinmu.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

“Idan kun lura, Ubangiji ne ya kare mu a yau. Babu irin harbin da ba su yi ba yau amma Ubangiji ya tsare mu.
“Za mu yi iyakar kokarinmu na samar da zaman lafiya don jami’a ba za ta ci gaba ba ba tare da jama’an gari ba.
“Za mu yi iyakar kokarin ganin mun samu fahimtar juna tsakaninmu da mutane.
“Mun dade muna yin hakan. Kuma muna ta cin nasarori tsawon shekaru. Duk da halin da ake ciki mai tsanani ne.”

An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga

A wani labari na daban, Shugaban karamar hukumar Wushishi da ke jihar Neja, Danjuma Suleiman Nalango, ya umarci a rufe makarantun gwamnati na firamare, sakandare da jami’o’i da ke karamar hukumar bisa shirin kai farmakin ‘yan bindiga makarantu don garkuwa da yara a Zungeru da garuruwa masu makwabtaka dasu.

Shugaban karamar hukumar ya sanar da wakilin Daily Trust ta wayar salula cewa akwai bayanan sirri da suka samu akan shirin masu garkuwa da mutane na kai wa foliteknik din jihar Neja da makarantar mata ta gwamnati da ke wajen Zungeru.

Kara karanta wannan

‘Yan banga sun ceto wasu Bayin Allah da aka yi garkuwa da su, har da jariri ‘dan wata 5

Asali: Legit.ng

Online view pixel