Da duminsa: An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga

Da duminsa: An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga

  • Shugaban karamar hukumar Wushishi da ke jihar Neja, Danjuma Suleiman Nalango, ya umarci a rufe makarantun firamare, sakandare da na jami’o’i da ke karamar hukumar
  • Hakan ya biyo bayan farmakin da ‘yan bindiga su ke ta kaiwa makarantun su na yin garkuwa da yara a Zungeru da wasu garuruwan masu makwabtaka da su
  • Shugaban karamar hukumar ya sanar da manema labarai ta waya cewa an samu bayanan sirri akan ‘yan bindiga suna shirin kai farmaki wasu makarantu da ke wajen garin Zungeru

Niger - Shugaban karamar hukumar Wushishi da ke jihar Neja, Danjuma Suleiman Nalango, ya umarci a rufe makarantun gwamnati na firamare, sakandare da jami’o’i da ke karamar hukumar bisa shirin kai farmakin ‘yan bindiga makarantu don garkuwa da yara a Zungeru da garuruwa masu makwabtaka dasu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

Shugaban karamar hukumar ya sanar da wakilin Daily Trust ta wayar salula cewa akwai bayanan sirri da suka samu akan shirin masu garkuwa da mutane na kai wa foliteknik din jihar Neja da makarantar mata ta gwamnati da ke wajen Zungeru.

Da duminsa: An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga
Da duminsa: An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce sun dauki wannan matakin ne don gudun lamarin da ya faru a Tegina inda aka yi garkuwa da daliban Islamiyya.

“Mun dauki matakin rufe makarantun ne don gudun lamarin ta’addanci ya auku a karamar hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jami’an tsaro sun sanar da mu cewa har gwamnan sun sanar akan shirinsu na kai farmaki makarantar yara da ke karamar hukumata.
“A bayanin da su ka yi, sun yi nuni da Zungeru a matsayin daya daga cikin wuraren da su ke shirin kai farmaki.
“Duk da dai jiya na samu bayanai akan yadda aka kama wani shugabansu, amma sun yi bayani akan lallai za su kai farmakin.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

“Don haka a matsayinmu na wakilan jama’a, wajibi ne mu dauki matakai sannan mu tabbatar jami’an tsaro sun jajirce kafin a samu matsala.
“Ba za mu bari abinda ya faru a Tegina ya maimaita kansa ba. Don haka muka rufe makarantun kudi,” a cewar shugaban.

Ya ce ya gane yadda mutane za su takura musamman yanzu da ake shirin yin jarabawar canja aji, amma gara da a dakatar da karatun don gudun su kai farmaki don da rana su ke zuwa kuma su kan kai su 300.

Idan har ‘yan bindiga su ka sanar da batun kai farmakinsu, tabbas sai sun kai. Don ya ce sun ga yadda lamarin Zungeru ya auku.

‘Yan bindiga sun dade suna barazanar kai farmaki Zungeru a cikin kwanakin nan. Kwanan nan su ka yi garkuwa da sakataren ma’aikatar sufuri ta jihar Neja.

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ya ja kunne akan kada shugabannin addinai da 'yan siyasa su mayar da matsalar tsaron Najeriya ta siyasa.

Ana ta samun karin rashin tsaro, ta’addanci da sauran ayyukan assha yayin da ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda su ke cin karensu babu babbaka a arewa maso yamma, arewa maso gabas da sauran bangarori.

Akwai mutane da dama da aka halaka, aka yi garkuwa da su sannan wasu aka yi musu fyade, Channels TV ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel