‘Yan banga sun ceto wasu Bayin Allah da aka yi garkuwa da su, har da jariri ‘dan wata 5

‘Yan banga sun ceto wasu Bayin Allah da aka yi garkuwa da su, har da jariri ‘dan wata 5

  • Rundunar Amotekun ta yi kokari wajen ceto wasu mutane da ‘yan bindiga suka dauke a jihar Ondo
  • Kafin a je ko ina, wadannan ‘yan banga na sa-kai, suka shiga jeji, suka kubuto da wadanda aka sace
  • Wani ‘dan bindiga ne ya yi shigar mata, ya shiga coci ya dauke har da uwa da ‘yar ta mai wata biyar

OndoJaridar Vanguard tace jami’an tsaron Amotekun, sun ceto wasu mutum biyar da ake zargin ‘yan biniga sun yi garkuwa da su a birnin Akure, jihar Ondo.

Wadanda aka kubutar sun hada da wata dattijuwa ‘yar shekara 78 da ta kafa coci a Akure, da kuma wani jariri mai wata biyar da haihuwa, da mahaifiyarsa.

Jagoran ‘yan bindigan, Abiodun lgbekele ne ya yi shigar 'yan mata, ya shiga wani coci da ke garin Akure, ya sace Bayin Allah yayin da suke ibada cikin dare.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa

Shugaban dakarun Amotekun, Adetunji Adeleye, ya bayyana cewa bayan awa da yin wannan ta’adi, rundunarsa ta cafke wadanda suka yi danyen aikin.

‘Yan banga
Jami'an Amotekun Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Abin da ya faru - Amotekun

“A ranar Laraba da kimanin karfe 11:15 na dare, mu ka samu kira cewa ‘yan bindiga sun dura cikin harabar coci, sun dauke wasu masu bautar Allah.”
“A ‘yan mintuna, dakarunmu suka shiga aiki, su ka kutsa jeji, suka bi duk wani lungu a kan titi, suka kama wani da ya yi shigar mata, ya sace mutane.”
“Sun ci zarafin matan da suka dauke, suka shiga da su jeji, a nan muka cafke su. Mun iya kubutar da mutane uku bayan awa daya mu na lalubensu a daji.”
‘Wani daga cikinsu ya amsa cewa su na cikin wadanda suka kware a satar mutane.” - Adetunji Adeleye.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan Sanda ke taimakawa ‘Yan bindiga a Arewa – Shugaban Majalisa yayi tonon silili

Aikin Operation Clean Up ya na kyau

Tribune ta rahoto Adetunji Adeleye yana cewa a aikinsu na ‘Operation Clean Up’, sun yi ram da gawurtattun masu laifi sama da 75 da suka addabi al’umma.

Bayan samun labarin za a kawo hari a yankin, Amotekun ta tashi-tsaye domin kare al’umma. A haka ne aka kama yaran da suka yi wa mutane kwacen waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel