Bincike: Yadda ‘yan majalisun Najeriya suka karkatar da sama da Naira biliyan 5.2 a 2019

Bincike: Yadda ‘yan majalisun Najeriya suka karkatar da sama da Naira biliyan 5.2 a 2019

Ba bakon lamari bane a samu batan kudade a hukumomin gwamnati a Najeriya. A wannan bincike, an bayyana yadda aka samu barakar makudan biliyoyi daga majalisar wakilai ta Najeriya a shekarar 2019

Abuja - Wani rahoton bincike ya nuna cewa, a shekarar 2019, ‘yan majalisar wakilai sun kashe sama da Naira biliyan 5.2 a lokuta daban-daban kan ayyuka daban-daban.

Wadannan kashe-kashe sun hada da kudaden tafiyar da lamurra na wasu ‘yan majalisa zuwa kudaden da aka kashe wajen gyare-gyare da kulawa ta yau da kullum, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Majalisar wakilai ta Najeriya
Bincike: Yadda ‘yan majalisun Najeriya suka karkatar da sama da Naira biliyan 5.2 a 2019 | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Facebook

Sai dai, ba a iya gabatar da lissafin inda aka kashe kudaden ba, kuma babu wata shaida da ta nuna inda aka yi amfani da kudaden.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

Baya ga haka, majalisar ta kuma zuba wasu kudade a wani asusun albashi, ba tare da takardun biyan kudi ba, kamar yadda ka'idoji na yau da kullum suka tanada.

Cikakkun bayanai na wadannan kashe-kashe da majalisar ta yi na kunshe ne a cikin rahoton shekara na babban oditan kudi na tarayya (AGF) na shekarar 2019.

Majalisar na daga cikin ma’aikatu da sassa da hukumomi (MDAs) na gwamnatin tarayya da babban oditan kudi ya tuhuma kuma ya kalubalanta kan kashe-kashen.

Wasu daga cikin tuhume-tuhumen sun hada da biyan kudaden ritaya ba kan ka'ida ba da kuma bayar da tallafin tsabar kudi sama da yadda aka kayyade da biyan kudi ba tare da takaddun shaida ba.

Babban oditan, a cikin rahoton, ya ce wadannan laifuffukan kudi na iya bayyana a matsayin asarar kudaden gwamnati da/ko karkatar da kudaden gwamnati ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kasafin kudin shekarar 2022 ya samu gagarumin koma baya a Majalisa

A cikin rahoton, babu amsa kan tuhume-tuhumen da babban oditan ya gabatar ko dai ta bangaren majalisar ko kuma mahukuntan majalisar dokokin kasar.

Tambayoyin da ya gabatar

Babbar danbarwar da aka gano a cikin takardun majalisar shine yadda ta baiwa mambobinta Naira biliyan 2.55 a matsayin kudin tafiyar da lamurra tsakanin watan Yuli zuwa Disamba 2019, kamar yadda.

Kudaden da aka biya a yankuna sun hada da:

  1. Arewa maso Gabas - miliyan 187
  2. Kudu maso Kudu - miliyan 272
  3. Kudu maso Gabas - miliyan 442
  4. Arewa ta Tsakiya – miliyan 391
  5. Kudu maso Yamma – miliyan 629
  6. Arewa maso Yamma – 629 miliyan.

Duba da bambance-bambancen, an bukaci magatakardar majalisar da ya bayar da dalilan kashe kudaden da suka kai Naira biliyan 2.55 da kuma aika su ga baitul mali.

Sannan kuma a mika shedar aika kudi ga kwamitocin asusun gwamnati na majalisar dokokin kasar idan ba haka ba su fuskanci hukuncin da ya dace.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

A wata tuhumar, ya ce majalisar ta baiwa ma’aikata 59 Naira miliyan 258 duk dai a majalisar.

Dangane da haka, an nemi magatakarda da: ya ba da dalilan da yasa hakan ta faru; ya gano kudin da aka kashe ba bisa ka'ida ba na Naira miliyan 258; da kuma mika su ga taskar gwamnati.

An kuma ce an bai wa wasu ma’aikata biyu Naira miliyan 107 don “gyara da kuma kula da wuraren zama da ba a bayyana ba.

Don haka, an bukaci magatakarda ya yi lissafin kudaden da suka kai Naira miliyan 107.9 da aka bayar ba bisa ka'ida ba; da dawo dasu kuma ya mayar dasu taskar gwamnati.

Akwai sauran badakala

A cikin shekarar ne majalisar ta mika kudaden da suka kai Naira biliyan 1.6 ga hukumomin kudaden shiga, tsakanin watan Fabrairu zuwa Disamba 2019.

Biyan dai ya hada da Pay As You Earn (PAYE) daga mutane shida, da karbar lamunin mota daga mutane biyar, da lamunin gidaje da aka karbo daga mutane shida a kan Naira miliyan 488, Naira miliyan 401.2 da kuma Naira miliyan 705.4, bi da bi.

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

Anan ma, an biya kudaden ba tare da amincewa daga hukumomin kudaden shiga da suka dace ba, wanda hakan ya saba wa Sakin layi na 220 (i) na Dokar Kudi.

Yayin da aka tuhume shi kan wannan, an bukaci magatakardar da ya dawo da kudaden zuwa baitul mali; jimillar Naira biliyan 1.6.

An kuma gano wasu Naira biliyan 1.01 da aka biya daga wani asusun albashi.

An biya kudin ba tare da shirya takaddun biyan kudi ba kamar yadda ka'idoji masu yawa suka bukata.

Hakazalika, dangane da haka, an bukaci magatakarda da ya ba da dalilan kan wadannan kudade tare da gabatar takardar biyan kudi ba.

An kuma bukace shi da ya yi lissafin zunzurutun kudin har Naira biliyan 1.01, ya aika dasu ga baitul mali, sannan ya mika shedar hakan ga kwamitocin asusun gwamnati na majalisar dokokin kasar.

Majalisar kasa, musamman kwamitinta na asusun gwamnati, ta shahara wajen yin magana mai tsauri da kuma yin barazana (ciki har da umarnin sammacin kamu) ga MDAs a duk lokacin da aka gurfanar dasu.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

Sai dai, barazana ce ba a daukar mataki

Kwamitin asusun gwamnati na majalisar dattawa, a lokuta da dama, ya yi barazana ga shugabannin manyan hukumomi kamar Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, Babban Bankin Najeriya, Ministan Labarai da Hukumar Raya Yankin Neja Delta.

Har ma kwamitin ya yi barazanar ba zai amince da kasafin kudin na wadannan MDAs ba amma duk a banza, kamar yadda Premium Times ta kawo a baya.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya kuma yi barazanar zayyana, kunyata da kuma gurfanar da MDAs da suka gaza yin abinda ya dace.

Sai dai kuma rahoton binciken da aka fitar ya tuhumi majalisar, ‘yan Najeriya suna jira su ga yadda ‘yan majalisar za su magance abubuwan da aka nuna.

Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022

A wani labarin, ’yan Najeriya na shirin shiga tsaka mai wuya a shekarar 2022, shekarar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke gab da barin Aso Rock.

Kara karanta wannan

Rahoto: Kudurorin gwamnatin Buhari da zasu jefa 'yan Najeriya cikin bakaken wahalhalu a 2022

Yayin da gwamnatin Buhari ke neman karin kudaden shiga domin biyan basussukan da ke kara yawa, za ta kwakule aljihun ‘yan Najeriya a shekara mai zuwa.

Gwamnati ta ci gaba da kokawa da cewa tana da karancin albarkatun kasa don bi da yawan jama'a da ke kara yawa a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel