Rahoto: Yadda rashin tsaro ya halaka 'yan sandan Najeriya 322, sojoji 642 a shekara 1

Rahoto: Yadda rashin tsaro ya halaka 'yan sandan Najeriya 322, sojoji 642 a shekara 1

  • Abin ban tsoro mai kama da bikin zubar da jini ya faru yayin da a cikin shekara daya aka halaka fiye da ‘yan sanda da sojoji 964 a cikin shekera daya
  • Bisa binciken jami’an sirri, a ranar Alhamis sun bayyana yadda aka halaka ‘yan sandan yayin farmaki daban-daban tsakanin watanni 3 na karshen 2020 da watanni 9 na 2021
  • Sakamakon yadda rashin tsaro ya ke ta hauhawa a kasar nan, har sojoji ne suka koma bayar da tsaro a bangare daban-daban na kasar nan

Lamari mai kama da bikin zubar da jini ya auku a kasar nan inda aka halaka fiye da ‘yan sanda da sojoji 964 yayin mayar da hare-hare cikin shekara daya, kanar yadda binciken sirrin SB Morgan su ka ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

Rahoton wanda ma’aikatar binciken sirrin ta gudanar a ranar Alhamis ta gano yadda kisan ya auku tsakanin watanni ukun kashen shekarar 2020 da watanni taran farkon shekarar 2021.

Rahoto: Yadda rashin tsaro ya halaka 'yan sandan Najeriya 322, sojoji 642 a shekara 1
Rahoto: Yadda rashin tsaro ya halaka 'yan sandan Najeriya 322, sojoji 642 a shekara 1. Hoto daga tthecable.ng
Asali: UGC

A cikin ‘yan shekarun nan, rashin tsaro ya nunku a bangarori daban-daban na kasar nan. An samu matsaloli irin na garkuwa da mutane, ta’addanci, fashi da makamai, rikicin manoma da makiyaya da sauransu.

Don kawo karshen wadannan matsaloli, sojojin kasar nan yanzu sun ja ragamar tsaro a yankuna daban-daban na kasar nan musamman a arewacin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin tsokaci akan matsalar tsaro, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin jawabinsa na ranar bikin ‘yancin kai, ya ce a watannin da suka gabata bangarori daban-daban na kasar nan sun jigata.

“Fiye da watanni 18 da suka gabata su ne datsi mafi wahala a tarihin kasar nan. Tun daga yakin basasa, ba na tunanin akwai wani lokaci da aka fuskanci matsaloli kamar yadda yanzu ake,” inji Buhari.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

A rahoton, an halaka jami’an tsaro 642 na sojin Najeriya da kuma 322 na ‘yan sanda duk a wannan datsin.

Hatta jami’an NSCDC da na kwastom ba su tsira ba.

Sauran wadanda ya shafa akwai jami’an DSS guda biyu, jami’an hukumar kula da shige da fice guda biyu sai hukumar kula da hatsarin kan titi guda daya.

Duk da dai rahoton bai bayyana yawan fararen hulunan da aka halaka ba cikin wannan datsin, amma an samu bayanai akan yadda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Har ila yau, an halaka ‘yan bindiga 1989 cikin wannan lokacin, wanda 973 daga ciki ‘yan Boko Haram ne sauran 290 kuma ‘yan kungiyoyi ne da suka kai farmaki.

An rasa a kalla ‘yan sa kai 129, ‘yan IPOB 100 da wasu sojojin guda 9.

Akwai ‘yan fashi 99 da aka halaka, masu garkuwa da mutane 88 da ‘yan sumogal 9.

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

A wani labari na daban, Tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Soji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma'a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura 'yan ta'addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.

A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel