Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta amince da karin kaso mai tsoka a tsarin albashin 'yan sanda domin gyara aikin na 'yan sanda
  • Sanarwar karin dai ya fito ta bakin ministan 'yan sanda, Muhammad Dingyadi a yau Labara a babban birnin tarayya
  • Shugaba Buhari dai ya kara albashin na 'yan sanda ne don kara musu gwarin giwa wajen aiwatar da ayyukansu

Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da karin 20% cikin 100% na albashin ma’aikatan rundunar ‘yan sandan Najeriya, Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati a Abuja ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda shugaba Buhari ya jagoranta.

Ministan 'yan sanda, Muhammad Dingyadi
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Buhari ta kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda | dailytrust.com
Asali: Facebook

Ya kara da cewa karin zai fara aiki daga watan Janairun 2022.

A cewar Dingyadi, karin ya samo asali ne daga batutuwan da aka taso dasu yayin zanga-zangar #EndSARS a watan Oktoba 2020.

Ya ce matakin na da nufin kara kwarin gwiwar jami’an ‘yan sanda a fadin kasar nan.

A cewarsa, karin kudin da ake samu na daya daga cikin hanyoyin inganta alaka tsakanin rundunar da al’ummar Najeriya.

Ya ce majalisar ta kuma amince da sake duba alawus-alawus din ‘yan sanda na yawon bude ido da alawus-alawus na canjin aiki zuwa kashi shida cikin dari, da kuma fitar da naira biliyan 1.2 domin biyan kudaden alawus din da ba su da inshora.

Ministan ya ce an amince da Naira Biliyan 13.13 a matsayin alawus na mutuwa ga ma’aikata 5,472. Sai dai ya ce za a fara biyan kudin ne kawai bayan da babban mai binciken kudi na tarayya ya binciki lamarin kuma ya amince.

Dingyadi ya kuma sanar da rage harajin N18.6bn ga kananan ma’aikata. Wannan dai ba zai kasance karo na farko da shugaban kasar ke amincewa da karin albashin ‘yan sanda ba.

A bangare guda, Channels Tv ta ruwaito cewa, Ministar Kudi Zainab Ahmed, ta bayyana cewa ba a samar da sabon tsarin albashin a kasafin kudin shekarar 2022 ba, kuma ma’aikatarta za ta jira sakamakon tantance kididdigar da aka yi daga babban Odita Janar.

Ahmad Lawan ya fadi sirri, ya bayyana albashin sanatoci da 'yan majalisun Najeriya

A wani labarin, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, ya bayyana albashin ‘yan majalisar tarayya da kuma kudaden alawus-alawus da ake biyansu.

Lawan ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ce ya zarce magabatansa wajen amincewa da kudirin doka.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a cikin wata makala da aka gabatar a jerin lakcocin ‘yan majalisa na farko da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokuradiyya ta kasa ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel