DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

  • Hukuma tsaro ta farin kaya ta bayyana wani sabon yunkuri na daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane
  • Hakazalia, DSS ta bayyana akwai yiyuwar fara farautar 'yan majalisa da ke tafiya hutu a lokacin kirsimeti
  • Hukumar ta kuma magantu kan jita-jitan cewa ana cin zarafin Nnamdi Kanu a gidan yarin da yake tsare

Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta jawo hankalin jama’a kan wani shirin daukar dalibai aikin ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, fashi da makami dakuma laifukan satan kudi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kakakin hukumar ta DSS, Dr Peter Afunanya ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata 14 ga watan Disamba.

Jami'an hukumar tsaron farin kasa ta DSS
DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Hukumar ta DSS ta ce baya ga dalibai, ‘yan Majalisar Dokoki/Majalisun Jihohi da ke hutu da sauran ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke hutu na iya fuskantar barazanar tsaro daban-daban.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

Da take magana kan kungiyar ta IPOB da kuma cin zarafin Nnamdi Kanu, hukumar DSS ta musanta dukkan zarge-zargen da kungiyar ta IPOB ke yi, inda ta bayyana cewa, ba a ci zarafin Kanu a gidan yari ta kowace hanya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

An kama wasu mutane 30 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aikata laifuka a jihar Imo, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

An kama barayin ne a wani samame da rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro suka kai a sansanoninsu da ke yankunan Orsu da Uli a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Wani basaraken gargajiya da aka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Okigwe ranar Lahadi, Acho Ndukwe na yankin Ihube mai cin gashin kansa, shi ma an ceto shi a yayin farmakin.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu na cikin walwala da nishadi, babu yunwan da yake ji, DSS tayi martani

Wannan samame dai na zuwa ne mako guda bayan da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC ta kwato bindigogi kirar kasashen waje guda 33, masu sarrafa kansu da kayan aikin tsaftace bindigu guda 15 daga wata maboyar ‘yan ta’adda a jihar Imo.

Dalla-dalla kisan mutane 3,125, da sace 2,703 a cikin watanni 11 a Arewa

A wani labarin, a wani abin da zai ci gaba da ba wa ‘yan Najeriya bakin ciki, wani rahoto ya nuna cewa akalla mutane 3,125 ne ‘yan bindiga suka kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, tare da yin garkuwa da 2,703 a arewacin Najeriya a cikin watanni 11 da suka wuce.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an samu wadannan alkaluman ne daga wani shiri na hukumar kula da harkokin kasashen waje ta Amurka mai suna Nigeria Security Tracker.

Ya kuma kara da cewa rahoton yace an tattaro daga rahoton kwata-kwata da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar daga watan Janairu zuwa Satumba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: EFCC ta maka Fami Fani-Kayode a kotu bisa wasu laifuka 12

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.