Rikici ya ɓarke tsakanin yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina

Rikici ya ɓarke tsakanin yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina

  • Rahotannin dake fitowa sun bayyana cewa an fara takun saƙa mai tsanani tsakanin yan bindigan Katsina da na Zamfara
  • Wata majiya ta shaida cewa tawagar yan bindiga biyu sun hana baƙin yan bindiga shigowa yankunan su dake Batsari a Katsina
  • Hukumar yan sanda tace sam ba ta da masaniya amma zata bincika domin gano ainihin abinda ke faruwa

Katsina - Rikicin cikin gida tsakanin yan bindiga a karamar hukumar Batsari jihar Katsina da abokan adawarsu na jihar Zamfara na ƙara kamari.

Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa yan bindigan Batsari na kame duk wani ɗan bindiga da suka gani ya shigo yankinsu daga jihar Zamfara.

A cewar majiyar, ƙauyukan Nahuta, Madogara, Zamfarawa da Tashar Modibbo da sauran wasu ƙananan kauyuka duk suna karkashin ɗan bindiga, Abu Radda.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun Yan bindiga sun kuma sace wani Sarki a Najeriya

Yan bindiga
Rikici ya ɓarke tsakanin yan bindiga a jihohin Zamfara da Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kuma jagoran yan bindigan ya umarci yaransa su cafke duk wani bakon ɗan bindiga ko barawo da suka gani ya shigo yankunan.

Haka nan kuma Abdu Mai Komi, wani ɗan bindiga mai iko da yankunan Gobirawa, Garin Runji, Garin Yara, Kondatso da Yasure, shi ma ya haɗa kai da Abu Radda wajen kame duk wasu bakin yan bindiga da suka shigo.

Meya haddasa faɗa tsakaninsu?

Wani rahoto ya nuna cewa yaran wani ɗan Bindiga daga Zamfara, Dangote, su ke yawan kai hare-hare yankin Batagarawa a Katsina.

Sai dai a hanyarsu ta komawa gida, yaran Abu Radda da na Abdu Mai Komai suka yi musu kwanton bauna suka kashe na kashewa suka kwace dabbobin da suka sato.

Wasu daga cikin mazauna kauyukan dake yankim Ruma Tsohuwa sun shaida yadda tawagar yan bindigan biyu suka fafata da junansu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jami'an DSS da Yan Sanda sun rufe cibiyar Press Centre a jihar Kano

Majiyar tace:

"Bayan sun kwace shanu da makaman yan bindigan, sun raba a tsakanin su da wasu da suka taimaka musu."

A halin yanzun, rikicin ya yi ƙamari matuka ta yadda ba wanda ke yawo da bindiga don gudun kada a farmake shi.

Shin yan sanda san haka na faruwa?

Kakakin rundunar yan sanda resehn jihar Katsina, SP Gambo Isa, yace hukumar yan sanda ba ta da masaniya amma zata bincika domin gano gaskiya.

A wani labarin na daban kuma wasu Miyagun yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Zariya

Wasu yan bindiga sun sake sace mutum 5 a ƙauyukan Dallatu da Kasuwar Da'a dake Dutsen Abba a ƙaramar hukumar Zariya, jihar Kaduna.

Dailytrust tace wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan wasu yan bindiga sun tare babbar hanyar Zariya-Kaduna, kuma suka kashe mutum 3, suka sace wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel